Home Back

Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki, Sun Yi Kisa, Sun Kwashe Mutune 22 A Katsina

leadership.ng 2024/10/6
Ƴan Bindiga Sun Kai Farmaki, Sun Yi Kisa, Sun Kwashe Mutune 22 A Katsina

Ƴan bindiga ɗauke da muggan makamai sun kai farmaki a garin Runka da ke ƙaramar hukumar Safana inda suka kashe mutum 1 suka raunata da dama.

Rahotanni daga garin Runka na cewa ƴan bindigar sun yi wa garin ƙawanya ne cikin daren jiya asabar ɗauke da mugggan makamai inda aka yi hasashen cewa sun kai su 100.

Ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Safana a majalisar dokokin jihar Katsina Hon. AbdulJalal Haruna Runka ya tabbatar da haka a hira da wakinmu ta wayar tarho.

Hon. Runka ya ƙara da cewa ƴan bindigar sun yi zuwan bazata, a cewarsa, sai da suka shirya suka gayyato wasu ƙungiyoyin ƴan bindigar sannan suka kawo harin.

Ya kuma bayyana cewa, mutanen Runka sun gaya masa cewa ‘yan bindigar suna da yawa kuma ba a samu labarin kawo harin kamar yadda ake samu idan sun shirya irin wannan ta’asa ba.

Ya ƙara da cewa ƴan bindigar sun gayyato dabar ƙasurgumin ɗan ta’adan nan da ya yi ƙaurin suna wato Mohoɗinge, da Jan Kare da kuma dabar Mustapha.

Sauran sun haɗa ƴan ta’adda daga yankin Kunamawa da ke ƙaramar hukumar Ɗan Musa domin kawo harin a garin Runka ta ƙaramar hukumar Safana.

‘Kamar yadda muka samu labari, sun zo ɗaukar wasu mutane ne da aka ba su bayanan su, sai dai sun yi rashin sa’a ba su tarar da su ba, saboda haka zuwa yanzu sun tafi da mutane 22 amma ba a gama tantancewa ba”inji shi

Kazalika Hon. AbdulJalal Haruna Runka wanda ya yi bayanin cewa suna zargin akwai ma su ba ɓarayin dajin bayanan sirri wanda shi yasa mutanen Runka ba su ji labarin zuwan su ba, sai dai kawai suka gan su.

People are also reading