Home Back

Za mu tsunduma yajin aikin gargaɗi a Kano – Ƙungiyar Likitoci

dalafmkano.com 2024/7/3

Ƙungiyar likitoci da ke aiki da gwamnatin jihar Kano LAGGMDP, ta ce za ta tsunduma yajin aikin gargaɗi na makonni biyu, daga ranar 19 ga wannan wata na Yuni da ake ciki, idan gwamnatin jihar ba ta yi musu abinda suka nema ba.

Ta cikin wata sanarwar da shugaban ƙungiyar, da kuma sakataren ta Dakta Anas Idris, reshen jihar Kano suka sanyawa hannun a yau Alhamis, sun ce akwai buƙatar gwamnatin ta biya likitocin da ta ɗauka su 61 a shekarar da ta gabata albashin su na wata biyu wato Oktoba da November, da suka gabata.

Da yake ƙarin bayani sakataren ƙungiyar Dakatar Anas Idris, ya ce matuƙar gwamnatin bata biya buƙatun likitocin da ta ɗauka aikin ba, babu makawa za su tsunduma yajin aikin.

Dakta Anas Idris ya kuma ƙara da cewa akwai buƙatar gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin gwamna Abba Kabir Yusuf, ta yi duba akan tsaron lafiyar likitocin yayin da suke bakin aiki, domin kula da lafiyar su.

A cewar sa, “Hukumar kula da asibitoci na jihar Kano ta janye bata musu sunan da tayi akan wata likita da ake zargin tayi sakaci da aikin ta, ta cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar a ranar 13 ga watan Mayun da ya gabata, “in ji shi”.               

Wakilinmu Abubakar Sabo ya rawaito cewa, ko a kwanakin bayan ma sai da shugaban ƙungiyoyin likitocin na ƙasa ya zo nan Kano, domin ganin cewar an shawo kan matsalolin da suke fama dasu.

People are also reading