Home Back

'Yan Bindiga Sun Kai Ƙazamin Hari a Wurin Zaman Makoki, Sun Kashe Bayin Allah

legit.ng 2024/5/22
  • Ƴan bindiga sun kashe mutum uku yayin da suka kai farmaki wurin zaman makoki a jihar Enugu ranar Lahadi
  • Rahotanni sun bayyana cewa maharan, wadanda ake zargin fulani makiyaya ne sun sun kai harin ke ba zato ba tsammani
  • Har yanzun rundunar ƴan sanda ba ta ce komai ba kan lamarin wanda ya bar mutane cikin jimami da alhini

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Enugu - Wasu miyagun ƴan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe mutum uku a Ugwuijoro da ke kauyen Nimbo, ƙaramar hukumar Uzo-Uwani a jihar Enugu.

An tattaro cewa maharan sun kai wannan farmaki ne a yammacin ranar Lahadi kuma mutane da dama sun samu raunuka.

Sufetan ƴan sanda, IGP Kayode.
Yan bindiga da ake zargin fulani makiyaya ne sun kashe mutum 3 a Enugu Hoto: PoliceNG Asali: Facebook

Majiyoyi daga ƙauyen sun bayyana cewa ƴan bindigar sun kai hari kan masu zaman makoki da manoma, lamarin da ya ƙara jefa mutane cikin alhini da jimami.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin waɗanda aka kashe a harin sun haɗa da Okeh Simon Ugwu Oruku, Okeh Chukwuebuka, Julius Ogbonna Odiegwu da kuma Gabriel Ugwor Ezea.

Wani faifan bidiyo da jaridar The Nation ta gani ya nuna yadda mutanen ƙauyen suka tarwatse.

Wani mutumi da aka ji murnarsa a bidiyon ya bayyana cewa maharan sun mamayi mutanen ƙauyen ba zato ba tsammani, suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Ana iya ganin tebura da kujeru a watse a cikin harabar gidan inda masu zaman makoki suka taru tare da gawarwakin waɗanda aka kashe kwance cikin jini.

Miyagun ƴan bindiga sun taɓa kai mummunan farmaki kauyen Nimbo tun a shekarar 2016, inda mutane masu yawa suka rasa rayukansu.

Wannan labari dai ya ja hankalin mutane a lungu da sako na ƙasar nan a wancan lokaci.

Har yanzu da muke haɗa maku wannan rahoton rundunat ƴan sanda reshen jihar Enugu ba ta fitar da wata sanarwa ko amsa sakonnin da aƙa tura mata kan lamarin ba.

Nasarorin sojoji a mako ɗaya

A wani rahoton na daban dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda 216 kuma sun kama wasu miyagu 332 a samame daban-daban a faɗin ƙasar nan cikin mako ɗaya.

Mai magana da yawun hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ), Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

People are also reading