Home Back

"Kai Waye": Abba Kabir Ya Dauki Zafi Kan Kwamishinan Ƴan Sanda Game da Hana Hawan Sallah

legit.ng 2024/7/6
  • Gwamnatin jihar Kano ta magantu kan daukar matakin hana bukukuwan salla da kwamishinan 'yan sanda ya yi a jihar
  • Kwamishinan Shari'a a Kano shi ya kalubalanci kwamishinan ƴan sanda inda ya ke tambayar yaushe ya samu cikakken ikon da zai dauki wannan mataki
  • Wannan na zuwa ne bayan rundunar ƴan sanda a jihar ta haramta gudanar da bukukuwan salla a fadin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kalubalanci kwamishinan ƴan sanda kan matakin hana bukukuwan sallah a jihar.

Gwamnatin ta ce kwamishinan ba shi da karfin ikon da zai iya hana bukukuwan sallah a fadin jihar baki daya.

Kwamishinan Shari'a a jihar Kano, Haruna Isah Dederi shi ya tabbatar da haka inda hadimin Gwamnan Abba Kabir ya wallafa a shafin X yau Asabar 15 ga watan Yuni.

Kwamishinan ya zargi kwamishinan 'yan sanda a jihar da kin bin umarnin gwamnan a matsayinsa na shugaban tsaron jihar.

"Dole na yi wannan tambaya, waye yake neman wuce ikon shugaban tsaron jiha?."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda wasu sun take umarninsa tare da daukar matakai ba tare da amincewarsa ba ko kwamitin tsaro wurin hana bukukuwan Sallah."
"Ta yaya mutum a cikin hankalinsa zai hana bukukuwan sallah a Kano? Yaushe gwamnan jihar ya bar mukamin shugaban tsaron jiharsa?"
"Ta yaya za a ce Gwamna da kansa sai dai ya ga sanarwar a kafafen sadarwa, waye ya ke tunkuda Kwamishinan wurin wuce gona da iri?."

- Haruna Isa Dederi

Kano: Ƴan sanda sun hana hawan Salla

A wani labarin, kun ji cewa Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta haramta yin hawa a yayin gudanar da bukukuwan Babbar Sallah mai zuwa a jihar.

Rundunar ta bayyana cewa a yayin bikin babbar Sallah na bana, ba za a yi hawan Sallah ba kamar yadda aka saba.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, 13 ga watan Yunin 2024.

Asali: Legit.ng

People are also reading