Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Ta'addan ISWAP 11 a Borno
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kashe mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP guda 11 a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan ne a yankin Jongo da ke dajin Sambisa a ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.
Zagazola Makama, wani masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi ya ce dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan ta'addan ne a ranar Juma'a, 5 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai na CJTF, sun mamaye maɓoyar ƴan ta’addan ne a ranar 5 ga watan Yulin 2024.
Bayan samun nasarar hallaka ƴan ta'addan da sojojin suka yi, sun kuma ƙwato tarin makamai masu yawa daga maɓoyarsu.
Daga cikin makaman da suka ƙwato akwai harsasai guda 99 masu kaurin 7.62mm, da harsasai guda 19 na musamman masu kaurin 7.62mm, jigidar AK-4 guda uku, alburusai 47, bindigogi guda biyu da gurneti guda biyu.
Dakarun sojojin ba su samu asarar rai ko rauni ba yayin fafatawa da ƴan ta'addan, sai dai ɗaya daga cikin jami'an rundunar haɗin gwiwar ya samu rauni a yayin fafatawar.
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan ISWAP sun kashe masunta aƙalla 15 tare da jikkata wasu da dama a wani hari da suka kai a ƙaramar hukumar Kukawa a jihar Borno.
Ƴan ta'addan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10:40 na dare, a lokacin da masunta ke shirin kamun kifi da daddare a yankin Tumbun Rogo Kangarwa da ke ƙaramar hukumar.
Asali: Legit.ng