Home Back

Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Fasahohin Ai Na Kasa Da Kasa Na Shekarar 2024

leadership.ng 2024/6/29
Xi Jinping Ya Taya Murnar Bude Bikin Baje Kolin Fasahohin Ai Na Kasa Da Kasa Na Shekarar 2024

Yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murnar bude bikin baje kolin fasahohin kwaikwayon tunanin dan Adam wato AI, na kasa da kasa na shekarar 2024.

A cikin sakonsa, Xi Jinping ya bayyana cewa, fasahar AI muhimmin karfi ne dake ingiza gwagwarmayar bunkasa kimiyya da masana’antu a sabon zagaye, wadda kuma za ta samar da kyakkyawan tasiri mai zurfi ga bunkasuwar tattalin arziki da al’adun dan Adam a duniya. Ya ce Sin na dora muhimmanci matuka a wannan fanni, tana kuma fatan kara hadin gwiwa da kasashen duniya, ta yadda za su taka rawa wajen hanzarta bunkasa fasahar AI lami lafiya da ingiza bunkasuwar tattalin arzikin duniya da ma kara amfanawa al’umommin duniya baki daya.

An kaddamar da wannan biki ne yau Alhamis a birnin Tianjin na kasar Sin. Gwamnatocin biranen Tianjin da Chongqing na kasar Sin ne suka yi hadin gwiwa suka shirya bikin na wannan karo mai taken “Raya makomar duniya bisa fasahar AI ”. (Amina Xu)

People are also reading