Home Back

An Gano Yadda Ake Amfani Da Jiragen Sama Masu Zaman Kansu Wajen Haramtacciyar Harƙyalla

leadership.ng 2024/11/4
An Gano Yadda Ake Amfani Da Jiragen Sama Masu Zaman Kansu Wajen Haramtacciyar Harƙyalla

Ministan sufurin jiragen sama na ƙasa Festus Keyamo, SAN, ya fitar da wata sanarwa dangane da ayyukan da jiragen sama masu zaman kansu ke yi a Nijeriya ba tare da bin ƙa’ida ba, yana mai nuna damuwarsu kan shigarsu cikin haramtattun ayyuka kamar safarar kuɗi haramun da safarar miyagun kwayoyi.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da kwamitin mai mambobi takwas a Abuja, Keyamo ya jaddada buƙatar yin gaggawar daƙile waɗannan ayyuka. Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da kwamitin zai taka wajen sanya al’umma su sake amince wa da su a fannin sufurin jiragen sama, da tabbatar da bin ƙa’idojin tsaro, da kuma kawar da ayyukan da ba su dace ba.

Sabon kwamitin da aka kafa ƙarƙashin jagorancin Kaftin Ado Sanusi, ana so ne ya gudanar da cikakkiyar ƙididdigar jirage masu zaman kansu da ba na kasuwanci ba da kuma bincikar ayyukan masu ɗauke da takardar shaidar amfani da sararin samaniya (AOC).

Har ila yau aikin kwamitin ya haɗa da binciken dalilin da yasa jiragen haya ba bisa ƙa’ida ba suka ci gaba da kasancewa a Nijeriya duk da ƙa’idojin da ake da su da kuma tabbatar da sahihancin ma’aikatan jirgi masu lasisi da na bogi.

Bugu da ƙari, an ba wa kwamitin ikon bayar da ingantattun shawarwari don ɗaukar matakai da nufin daƙile ayyukan jirge marasa izini da kuma inganta sa ido kan jiragen sama masu zaman kansu a duk faɗin ƙasar.

A jawabinsa, Kyaftin Sanusi ya ce, a matsayinsa na shugaban kwamitin, ya nuna jin daɗinsa da damar da aka ba shi na magance waɗannan muhimman batutuwa. Ya tabbatar da ƙudirin kwamitin na yin bincike kan musabbabin ayyukan da suka shafi jiragen sama masu zaman kansu da kuma samar da tsauraran matakai da za su kare mutunci da tsaron sararin samaniyar Nijeriya.

People are also reading