Home Back

KISAN MUTUM 85 A WURIN MAULIDI: Hukumar Sojojin Najeriya za ta hukunta sojoji 12 da ta samu da laifi

premiumtimesng.com 2024/5/20
KISAN MUTUM 85 A WURIN MAULIDI: Hukumar Sojojin Najeriya za ta hukunta sojoji 12 da ta samu da laifi

Sojojin Najeriya 12 na fuskantar yanke masu hukuncin da Hukumar Sojojin Najeriya za ta yi, bayan samun su da laifin kai harin bam a ka masu maulidi, a ƙauyen Tudun Biri, cikin Ƙaramar Hukumar Igabi, a Jihar Kaduna.

Harin bam ɗin wanda aka kai ranar 3 ga Disamba, 2023, ya halaka mutum 85, wasu masu yawan gaske sun samu munanan raunuka.

Daraktan Yaɗa Labarai na Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya, Manjo-Janar Edward Buba, shi ne ya bayyana a wata ganawa da ya yi da manema labarai a ranar Alhamis, a Abuja.

Ya ce Hukumar Tsaro ta Sojoji za ta hukunta soja 12 ɗin da ta samu da laifin kai harin bam ɗin.

Ya ce an yi taka-tsantsan wajen ɗaukar dogon lokaci ana zurfafa bincike, domin tabbatar da an gano masu laifi, kuma an yanke masu hukunci, domin hakan shi ne adalci ga waɗanda suka rasa rayukan su da waɗanda suka jikkata.

Ya ce amma ba zai iya ci gaba da wani ƙarin bayani ba, domin ba a kai ga yanke masu hukunci ba tukunna.

“Sojojin Najeriya za su ƙara yin taka-tsantsan sosai wajen kai hare-hare kan ‘yan ta’adda, domin tabbatar da cewa nan gaba ba a sake yin kuskuren kai hari a cikin fararen hula ba.”

People are also reading