Home Back

Man City Da Arsenal: Yadda Aka Yi Faɗuwar Guzuma A Wasan Da Aka Kece Raini A Etihad Etihad

leadership.ng 2024/4/30
Man City Da Arsenal: Yadda Aka Yi Faɗuwar Guzuma A Wasan Da Aka Kece Raini A Etihad Etihad

Manyan kungiyoyin kwallon kafa na kasar Ingila Manchester City da Arsenal sun buga kunnen doki a wasan mako na 30 na gasar Firimiya da suka buga a filin wasa na Etihad da ke Birnin Manchester.

An yi tsammanin wasan tsakanin manyan kungiyoyin biyu ya yi zafi duba da cewa dukkansu suna fatan ɗarewa saman teburin Firimiya na bana yayinda ake gab da kammalawa.

Amma kowane bangare ya jajirce domin ganin ya hana abokin karawarsa jefa kwallo ko ɗaya a ragarsa, inda hakan kuma ya sa Liverpool ta koma matsayi na daya a kan teburin gasar bayan ta doke Brighton a Anfield.

 
People are also reading