Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum Ya Rasu? Gaskiya Ta Bayyana
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - A yau Laraba, 5 ga watan Yuni mutane suka fara yaɗa jita jitar cewa Allah ya yiwa Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum rasuwa.
Masu ƴada jita jitar suna rubutu ne tare da sanya hoton wata mota da ake ganin tana da alaka da malamin.
Sai dai Sheikh Guruntum ya bayyana gaskiyar abin da ya faru a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Guruntum ya bayyana cewa asalin abin da ya faru shi ne yaronsa ne ya yi hatsari sai mutane suka rika ɗaukan hoton motar suna cewa shi ne ya mutu.
Duk da haka malamin ya bayyana cewa yaron na shi yana cikin koshin lafiya saboda bai ji rauni ba a sanadiyyar haɗarin.
Biyo bayan yada jita jitar malam ya mutu, ya karyata labarin tare da yin nasiha ga masu ƴaɗa labarin ƙanzon kurege.
Malam Guruntum ya ce ya kamata mutane su nisanci yada abin da ba su da tabbas da cewa ya faru.
A karshe malamin ya yi kira ga al'ummar Musulmi da su kwantar da hankulansu domin komai yana tafiya daidai tattare da rayuwarsa.
Sheikh Ahmad Tijjani Yusuf Guruntum shahararren malamin addinin Musulunci ne da ya fito daga jihar Bauchi.
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kungiyar Jama'atu Izatil Bidi'a Wa Ikamatis Sunnah, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kai dan agaji Hajji.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yi alkawarin kai dan agajin zuwa Hajji ne yayin da ya tsinci makudan kudi kuma ya maido su ga mai su.
Asali: Legit.ng