Home Back

RIKICI KAN WURIN ZAMA A MAJALISAR DATTAWA: ‘Mu tsoffin ‘yan-alewa ne, ba sabbin-yanka-rake ba’ – Sanata Goje, Ya’u

premiumtimesng.com 2024/5/19
RIKICI KAN WURIN ZAMA A MAJALISAR DATTAWA: ‘Mu tsoffin ‘yan-alewa ne, ba sabbin-yanka-rake ba’ – Sanata Goje, Ya’u

Sanatocin Najeriya sun koma Majalisa bayan shafe hutun Easter da na Ƙaramar Sallah fiye da makonni huɗu a gida. Sun koma inda suka fara zama a gyararren Zauren Majalisar Dattawa, wanda ya shafe shekaru biyu ana gyaran sa.

Yayin da za a fara zaman farko a sabon Zauren Majalisa a ranar Talata, sanatocin su 109 dai kowane ya taras an ware masa wurin zaman sa, har da Shugaban Majalisar Dattawa.

Sai dai kuma wasu manyan sanatoci sun nuna damuwa tare da raina wurin zaman da aka ware masu, wanda suke ganin bai dace a ce a wurin za su zauna ba.

Sanatocin da suka nuna ɓacin rai na su, sun ce a matsayin su, bai kamata a ba kowanen su kujera a wuraren da aka ware masa a ce nan ne wurin zaman sa a Majalisa ba.

Daga nan sai suka nemi a maida su can a gefen dama, kuma a sahu na farko, daidai inda za su riƙa yin ido-huɗu da Shugaban Masu Rinjaye, Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa da kuma Shugaban Majalisar Dattawa.

Biyu daga cikin Sanatocin da suka yi hayaniya, su ne Sanata Ɗanjuma Goje, ɗan APC daga Jihar Gombe, sai kuma Sanata Sahabi Ya’u, ɗan APC daga Jihar Zamfara. Sun yi ta ɗaga murya sosai su na nuna ƙin amincewa da wurin zaman da aka ware masu.

Sanata Sahabi Ya’u ya fusata, har ya tunkari Shugaban Masu Rinjaye, Opeyemi Bamidele, domin ya nuna rashin amincewa.

An ji shi ya na cewa wurin zaman da aka ware masa, can a ɓangaren dama a sahu na biyu, bai dace da shi ba, kuma babu daɗin zama, ga shi kuma daɗaɗɗen sanata ne, ba sabon-shiga ba ne.

Shugaban Marasa Rinjaye ya yi ƙoƙarin tausasa Sahabi, amma bai yi shiru ba.

Shi ma Sanata Goje daga Jihar Gombe, ya tunkari Shugaban Masu Rinjaye, ya ce masa inda aka ware masa a sahu na biyu bai dace da shi ba, a matsayin sa na babban sanata. Nan take ya nemi a sauya masa wurin zama.

Daga nan ne dai wuri ya ruɗe, har wajen minti 30. Sai da ta kai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya sa baki, ya nemi kowa ya yi shiru, kuma ya zauna.

Waɗanda ake kira Manyan Sanatoci su ne waɗanda suka yi fiye da zango ɗaya a majalisa, wato tsoffin-‘yan-alewa.

Su kuwa sabbin-shiga majalisa a karon farko, su ake kira sabbin-shiga, ko sabbin-yanka-rake.

Kakakin Majalisarar Dattawa, Yemi Adaramodu ya ƙi bai wa abin da ya faru muhimmanci, ya ce hakan bai faru ba.

People are also reading