Home Back

Bayan Kisan Manoma 86 A Yankin Wasagu: Gwamnan Kebbi ya ce zai riƙa sa hannun zartas da hukuncin kisa kan masu yi wa ‘Yan bindiga leken asiri

premiumtimesng.com 2024/5/19
Bayan Kisan Manoma 86 A Yankin Wasagu: Gwamnan Kebbi ya ce zai riƙa sa hannun zartas da hukuncin kisa kan masu yi wa ‘Yan bindiga leken asiri

Gwamnan Jihar Kebbi Nasiru Idris ya tabbatar da cewa zai riƙa gaggauta sa hannun zartas da hukuncin kisa kan duk wani ‘infoma’ mai yi wa ‘yan bindiga leƙen asiri a faɗin jihar.

Gwamna Idris ya yi wannan kakkusan gargaɗi a ranar Asabar, lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya da jajentawa ga mazauna garin Tudun Bichi, ƙauyen da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Danko-Wasagu.

Ya je ne domin yi masu ta’aziyyar kashe-kashen da ‘yan bindiga suka yi a garin, a hare-haren da suka riƙa kai masu, ba sai ɗaya ko sau biyu kaɗai ba.

Gwamnan ya nuna matuƙar ɓacin rai jin cewa, mafi yawa mutanen da ake tare da su ne ke aika wa ‘yan bindiga bayanan leƙen asirin dukkan hare-haren da suke kaiwa.

Ya ce, “ayyukan infomas’ masu yi mahara leƙen asiri ya kai maƙurar rashin imani. Kawai don a baka ɗan kuɗin da bai taka kara ya karya ba, sai kira ‘yan bindiga su kai hare-haren kisa a cikin ‘yan uwan ka.

“Ba zan taɓa sassautawa ko jin tausayin duk wani infoma ba. Tunda mutanen banza da wofi ne a cikin al’umma.

“Daga yau ina sanar da cewa duk ranar da kotu ta yanke wa ‘infoma’ hukuncin kisa, ni kuma zan gaggauta sa hannun zartas da hukuncin kisa a kan sa.”

Nan take ya amince da roƙon ya gyara hanya mai nisan kilomita uku daga Tudun Bichi zuwa cikin garin Wasagu, wadda ba ta biyuwa saboda lalacewar gada.

Tun da farko sai da Dagacin Tudun Bichi, Muhammad Mika’ilu ya gode wa gwamnan, ya ce shi ne gwamnan farko da ya taɓa kai ziyara garin.

Ya shaida masa cewa tsawon damina biyu kenan ‘yan bindiga sun hana su zuwa gona su yi noma.

“To yanzu ma gabatowar fara aikin gona, sai suka sake fara kawo masu sabbin hare-hare.

Ya roƙi a kai masu agajin jami’an tsaro masu manyan makamai kuma a gyara hanyar su ta zuwa Wasagu.

Wani dattijo mai suna Sani Manoma, ya shaida wa Gwamna cewa ‘yan bindiga sun kashe masu manoma 86 a hare-hare daban-daban da suka riƙa afkawa kan manoman da ke garuruwa daban-daban na yankin.

Ya ce a harin da aka kai na ranar Alhamis, mahara sun yi wa mutum 7 mummunan kisan-gilla.

People are also reading