Home Back

Matashiya Ta Kashe Kanta Ta Hanyar Shan Maganin Ƙwari A Delta

leadership.ng 2024/5/19
Matashiya Ta Kashe Kanta Ta Hanyar Shan Maganin Ƙwari A Delta

Wata matashiya mai suna Blessing, mai shekaru 34 a duniya ta hallaka kanta ta hanyar shan maganin kwari a garin Warri da ke Jihar Delta.

Sai dai har yanzu babu cikakken bayani game da dalilin da ya sa matashiyar ta kashe kanta.

Amma wata kawar matashiyar mai suna Ejiro, ta bayyana cewar ta kashe kanta ne sakamakon matsananciyar damuwa da ta shiga.

A cewarta: “Ta sayo maganin kashe kwari ‘Sniper’ ta shanye ba tare da kowa ya sani ba, sannan ta rubuta takarda ta ajiye a kusa da ita, a cikin takardar ta bayyana cewar ta shiga damuwa. Babu wanda ya taimake ta daga ‘yan uwa da abokan arziki.”

Zuwa lokacin hada wannan rahoto dai ‘yan uwan matashiyar sun birne ta.

Amma babu wata sanarwa a hukumance da jami’an tsaro a jihar, kan faruwar lamarin.

People are also reading