Home Back

Komai ya Tsaya Cak, Mamakon Ruwan Sama ya Wanke Unguwanni a Legas

legit.ng 3 days ago
  • Legas ta gamu da mamakon ruwan sama da aka shafe awanni ana yi, yayin da hakan ya dakatar da ayyuka a sassan jihar
  • Rahotanni sun bayyana cewa mamakon ruwan ya shanye tituna tare da ruguzo da gidaje da dama, a lokaci guda kuma an rufe shaguna
  • Dama a baya hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) ta yi jan kunnen cewa akwai yiwuwar mummunan ambaliyar ruwa a sassan kasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos- Bayan jan kunne da hukumar kula da yanayi ta kasa (NIMET) ta yi kan barkewar ambaliyar ruwa a Najeriya, a jiya ruwa ya mamaye jihar Legas.

Mamakon ruwan saman ya haddasa cunkosun ababen hawa yayin da hada-hada ta tsaya cak a yankuna da dama na jihar.

Babajide Sanwo Olu
Ruwa ya wanke jihar Legas Hoto: Babajide Sanwo-Olu Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta wallafa cewa ruwan kamar da bakin kwarya ya raba mazauna Ibeju-Lekki da muhallansu, yayin da kowa ke neman mafaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mamakon ruwan sama ya rusa gidaje

Ruwa kamar da bakin kwarya na aka yi a Legas na akalla awa 10 ya rusa gidaje da dama yayin da ruwan mamaye titunan jihar.

Jaridar Punch ta wallafa cewa mamakon ruwan ya rikito da gini mai hawa biyu a Mushin, yayin da dalibai su ka gaza zuwa makarantu.

A hukumance, gwamnatin jihar Legas ta bayyana cewa an shafe awa tara ana ruwan, sai dai wasu na ganin an shafe awanni 12 ana ruwan a yankunansu.

Wasu daga yankunan da lamarinya fi kamari sun hada da Iyana-Oworo, Agege, Ijegun-Isheri Osun, Gbagada, Lagos Island, Eredo, Bojije, Epe, Sangotedo, Ibeju-Lekki, Awoyaya, Labora da Abijon.

Ruwa ya rusa gidaje 100 a Filato

A wani labarin, kun ji cewa mamakon ruwan sama ya lalata gidaje sama da 100 a jihar Filato, inda mutane suka rasa matsugunasu a wasu yankunan.

Ruwan, wanda ya fi karfi a kananan hukumomin Jos ta Arewa da ta Kudu ya lalata rufin kwanon wasu gidajen, yayin da wasu kuma kofofin ne suka fita.

Asali: Legit.ng

People are also reading