Home Back

NDLEA Ta Kama Wani Fasinja Ɗauke Da Kwayar Tramadol 4,000 A Filin Jirgin Sama Na Legas

leadership.ng 2024/5/17
NDLEA Ta Kama Wani Fasinja Ɗauke Da Kwayar Tramadol 4,000 A Filin Jirgin Sama Na Legas

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wani fasinja dauke da kwayoyin tramadol 4,000 a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Ikeja, Legas.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ranar Lahadi a Abuja.

Babafemi ya ce jami’an NDLEA da ke kofar ‘C ‘ ta filin tashi da saukar jiragen sama na Legas a ranar Juma’a sun dakile yunkurin wani da ake zargi na fita da kwayoyi zuwa Malpensa, Italiya a cikin jirgin Ethiopian Airline.

Ya ce an gano sinadarin ne a boye a cikin tufafin mata da kuma wasu cikin kananun jakar baya.

People are also reading