Home Back

Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Rabon Kayayyakin Amfanin Gona Ga Manoman Kaduna 40,000

leadership.ng 2024/6/26
Gwamna Uba Sani Ya Kaddamar Da Rabon Kayayyakin Amfanin Gona Ga Manoman Kaduna 40,000

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya kaddamar da rabon kayayyakin amfanin gona ga kananan manoma 40,000 a karkashin shirin ‘A Koma Gona’, a fadin kananan hukumomin jihar 23.

Da yake jawabi ga manoma a wajen taron a ranar Litinin, gwamnan wanda ya bayyana jin dadin kasancewa tare da manoman ya ce, “noma shi ne kashin bayan tattalin arzikinmu, wanda ke samar da ayyukan yi da kuma tabbatar da dorewar rayuwa. Jihar Kaduna na da albarkar noma mai dimbin yawa.

Don haka, Gwamnan ya yi kira ga manoman da suka ci gajiyar shirin su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata.

Tun da farko a jawabinsa na maraba, Kwamishinan Noma, Murtala Dabo, ya ce, shirin da Gwamnan ya bullo da shi, ba wai zai inganta samar da abinci a Kaduna da Nijeriya kadai ba ne, zai taimaka matuka ga burin Gwamnan na farfado da tattalin arzikin karkara.

Sani

Shugaban karamar hukumar Ikara, Sadiq Ibrahim Salihu ya bayyana matukar godiya ga Gwamnan, inda ya ce, jajircewarsa na ci gaba da kyautata rayuwar manoma da masu sana’o’in noma, wanda ya kasance ginshikin rayuwar al’ummar Ikara da sauran mutanen kananan hukumomi a shiyyar.

People are also reading