Home Back

Najeriya: Cikar shekaru 25 na mulkin demokaradiyya

dw.com 2024/7/6
Hoto: Uwais Abubakar Idris/DW

 Tinubun da har ila yau ke cika shekara guda bisa mulki na kasar dai ya karya kummalo tare da wata ziyara ta ba zata zuwa zauren majalisun kasar guda biyu.In  da ko bayan wani jawabi ga masu takama da yin dokoki ga kasar, shugaban ya rattaba hannu bisa wata dokar sake dawowa bisa tsohon take na kasar. Masu mulki na kasar dai na fatan sake cusa kishi na kasa na iya kai wa ga sake farfadowar lamura a tsakanin miliyoyin al'umma na  kasar.

Bukatar jajircewa domin nuna kishin kasa don gina Najeriya

Kuma  Tinubun bai boye wa 'yan kasar bukatar sadaukar da kai a kokari na sake ginin tarayyar Najeriyar da ke tunanin girma amma a cikin rudani da kila ma rasa  imani bisa makoma ta kasar. Ba tare da wannan majalisa ba da kila ban samu hanyar kai wa zuwa ga shugabanci na kasar nan ba. Kuma ina rokon ku da ku cigaba da hada kai da mu domin ginin kasar mu. Ba mu da wani zabi,kasarmu ce. Babu wanda zai iya taimakonmu. Ba wani mutum , ko wata kungiya ko ma wata kasa da ke iya taimaka mana, sai mun yi da kanmu‘ Tsohon taken da ya mai da hankali ga kokari na cusa son kasa dai ya dauki lokaci yana jawo dagun hakarkari cikin kasar a tsakanin 'yan mulkin da ke fadin a koma baya, da kuma talakawan da ke fadin a karasa da koma.

Har yanzu dai jama'a na jiran ganin bunkasar tattalin arzikin Najeriyar

  Sanata Simong lalongda ke zaman dan majalisar dattawa ta kasar kuma shugaba na yakin zaben da ya dora Tinubun bisa mulki, ya ce miliyoyi na 'yan kasar na da bukatar sauyin kallo cikin batutuwan kasar a halin yanzu. Ranar ta yau dai na zaman damar gwada kwanji a tsakani na masu mulki na kasar da suka share lokaci suna nunin ayyuka na raya kasa a shekarar guda. Shekara guda da kamun mulki dai miliyoyin al’ummar taryyar Najeriyar dia na zaman jiran cikon alkawarin gina tattali na arziki

People are also reading