Home Back

Sanata Saliu Ya Raba Taki Da Injinan Ban Ruwa Ga Manoman Kwara

leadership.ng 2024/6/26
Sanata Saliu Ya Raba Taki Da Injinan Ban Ruwa Ga Manoman Kwara

 Shugaban kwamitin majalisar dattijai mai kula da ayyukan noma da raya karkara, Sanata Saliu Mustapha ya kaddamar da rabon taki buhu 3,500 mai nauyin kilogiram 50, ga kananan manoma a fadin kananan hukumomi hudu na gundumar mazabar Kwara ta tsakiya da yake wakilta a majalisar dattawa.

Sanatan ya ce rabon kayan shi ne matakin farko na dabarun da za a tabbatar da dorewar ayyukan noma a gundumar.

Wadanda suka ci gajiyar rabon kayan noman da dan majalisar ya yi sun hada da mambobin kungiyar manoma ta Najeriya AFAN, da daidaikun jama’a, da ‘ya’yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wadanda suke noma.

A lokacin rabon kayayyakin noman a filin wasa na hukumar raya kogin Neja ta karamar hukumar Ilorin, Mustafa ya ce, wasu karin manoma za su ci gajiyar shirin nan gaba kadan.

Sanata Saliu

Ya Kara da cewa shirin mai taken: “Tallafawa Manoman Kwara ta Tsakiya: Bude hanyoyin dogaro da kai wajen samar da abinci,” na da nufin tallafa ayyukan noma da habaka samun yabanya ga manoman mazabar.

“Tasirin sauyin yanayi da kuma yawaitar noman gonaki yana da illa ga ingancin kasar noma. Wannan ya haifar da raguwar amfanin amfanin gonar da ake samu.

“Yana da mahimmanci in jaddada cewa ni da kaina na sayi buhunan taki guda 3,500 da aka raba a yau domin karfafa wa manomanmu gwiwa da inganta amfanin gonakinsu,” in ji Sanata Mustafa.

Mustapha ya bayyana cewa rabon taki mai yawa irin wannan na nuni da yadda ake zuba jari mai yawa a fannin noma, wanda hakan ke nuna aniyar inganta samar da abinci da tallafawa rayuwar manoma domin bunkasa noman abinci a jihar.

Sanatan na Kwara ya yi amfani da wannan dama wajen nuna wasu daga cikin nasarorin da ya samu cikin shekara daya da shafe a matsayinsa na dan majalisa da ya hada da gudanar da aikin sake gina titi Mai tsawon kilomita daya a daura da Jami’ar Al-Hikmah wanda ya dangana da titin Oke zuwa Foma a karamar hukumar Ilorin ta yamma.

Sanata Saliu

Ya kara da cewa, an kuma gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana da sanya fitulun titi a fadin kananan hukumomin hudu na mazabar domin taimakawa kokarin gwamnatin jihar na ganin jama’a sun samu tsaftataccen ruwan sha.

People are also reading