Home Back

KISAN SOJOJI 17 A DELTA: Kwamitin Sojojin Bincike ya fara zaman sa

premiumtimesng.com 2024/5/16
RA’AYIN PREMIUM TIMES: Munin kisan gillar da tsagerun Delta suka yi wa sojojin Najeriya
Picture Crdt: Guardian Nigeria

Kwamitin Sojojin Bincike wanda Hedikwatar Tsaron Najeriya ta kafa, ya fara zaman binciken musabbabin kisan Sojojin Najeriya 17 da aka yi a yankin Okuama, cikin Ƙaramar Hukumar Ughelli ta Kudu a Jihar Delta.

Kwamitin ya fara zama a ranar Laraba, a Ƙaramin Gidan Gwamnatin Delta da ke Warri ta Kudu a Jihar Delta.

An dai shirya za a fara zaman da ƙarfe 2 na rana, amma ba a fara ba sai sai ƙarfe 3:45 na yamma.

An fara zaman tare da wasu masu ruwa da tsaki su shida daga yankin Okoloba da ke ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Bomadi.

Sai dai babu wakili daga yankin Okuama, inda aka kashe sojojin.

Amma kuma Daraktan Harkokin Siyasa da Tsaro a Delta, David Tonwe, wanda shi ne ya shigar da mutanen shida a wurin zaman, ya shaida wa manema labarai cewa ba a amince da zaman wakilan daga yankin Okoloba a ɗakin taron zaman kwamitin ba.

Makonni biyu da suka gabata ne dai Hukumar Sojojin Najeriya ta yi zargin cewa wssu sarakunan yankin Delta na da hannu wajen mummunan kisan soja 17.

Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, Christopher Musa, ya yi zargin cewa wasu sarakunan gargajiyar da ke yankin Okuama da kewaye a Jihar Delta, sun taka mummunar rawa wajen haɗa baki a kashe sojoji 17 a jihar.

An kashe sojojin ne a ranar 14 Ga Maris, a yankin Okuama.

Sai dai kuma Majalisar Sarakunan Jihar Delta, sun fitar da sanarwar neman sojoji su saki basaraken da ya miƙa kan sa ga ‘yan sanda, su kuma suka damƙai shi a hannun sojoji.

Sun bayyana cewa su da ɗan uwan su da ke tsare ba su da hannu a rikici da kashe-kashen da suka afku a yankunan ko kuma kisan sojoji 17.

To amma Janar Musa a wata tattaunawa da ya yi da Arise TV, a Abuja ranar Laraba, ya ce sarakunan ƙabilar Urhobo na da hannu a rikice-rikicen da kuma kisan sojoji 17.

“Ni mutun ne mai ganin girman sarakunan gargajiya da dattawa. To amma kuma sarakunan Urhobo su na da masaniyar dukkan abin da ke faruwa a yankunan su. Tun bayan mummunan kisan gillar da aka yi wa sojoji, a yankin a yanzu kuma ana samun yawaitar kashe mutane ana yin tsafe-tsafe da sassan jikin su. Hakan su na yi ne domin nuna cewa su na da ƙarfin da har sojoji ma kashewa suke yi.” Inji shi.

“Da yawan su sun san abin da ke faruwa, amma sun yi shiru. Mai yiwuwa shi ma Basarake Ikolo dake hannun mu ba ya cikin waɗanda suka yi kisa, to amma ya san abubuwan da ke faruwa a yankin, ya yi shiru da bakin sa.

“Kuma sarakunan ƙabilar Urhobo sun san makasan sojojin mu. Kuma wasun su suna cin moriyar ta’addancin da ɓatagarin yankin ke aikatawa.

“Kuma ko ma dai me kenan, ai bincike zai tabbatar da mai gaskiya da maras gaskiya.” Inji shi.

PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cews sojoji sun tasa ƙeyar basaraken soja 17 a masarautar sa, bayan ya miƙa kan sa hannun ‘yan sanda.

Sojojin Najeriya sun yi awon-gaba da basaraken masarautar Ewu, cikin Ƙaramar Hukumar Ighelli ta Kudu a Jihar Delta, bayan ya miƙa kan sa a hannun ‘yan sanda.

Basaraken mai suna Clement Ikolo dai sojoji ne suka ayyana cigiyar sa ruwa jallo tare da wasu mutum takwas da sojojin ke zargi suna da hannu a kisan-gillar soja 17 a ranar 14 Ga Maris a yankin Okuama.

PREMIUM TIMES ta ji cewa Ikolo ya kai kan sa hannun ‘yan sanda ne a jihar, a ranar Alhamis.

Sojojin Najeriya sun ɗauko Ikolo cancak a jirgin sojoji daga Delta zuwa Hedikwatar Sojojin Najeriya da ke Abuja, a ranar Juma’a.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Delta ta damƙa shi ga Sojojin Najeriya a ranar Juma’a, kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka tabbatar.

Kakakin ‘Yan Sandan Jihar Delta, Bright Edafe, bai amsa kiran da wakilin mu ya yi masa, kuma mai turo amsar saƙon tes da aka yi masa, domin ƙoƙarin jin ta bakin sa kafin a buga wannan labari.

An tabbatar da cewa wasu danƙara-danƙaran sojoji ne suka kai shi filin jirgin Delta, daga can jirgin kuma Air Peace ya ɗauke shi zuwa Abuja, wajen ƙarfe 9 na safe.

People are also reading