Home Back

Da Ma Sai Da Muka Gargadi Ƴan Nijeriya Kan Sake Zaben APC – Tambuwal

leadership.ng 2024/7/7
Da Ma Sai Da Muka Gargadi Ƴan Nijeriya Kan Sake Zaben APC – Tambuwal 

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana tsananin halin ƙuncin rayuwa da al’ummar ƙasa ke fuskanta a sakamakon sake zaɓen jam’iyyar APC a 2023. 

Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a Majalisar Dattawa ya bayyana hakan ne a yau Lahadi a wajen taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a Sakkwato.

Ya ce; “A lokacin yekuwar neman zabe a 2023, mun gargadi ‘yan Nijeriya kan kada su yi kuskuren sake zaben APC saman mulki domin ba su da wani abin kwarai da za su aiwatar masu.”

“Mun bayyanawa jama’a cewar APC ba ta shiryawa mulkin ƙasar nan ba. Abin da suke bukata kawai shi ne su karɓi mulki su shiga ofis. To yanzu sun karbi mulki kuma suna cikin ofis amma ba su san abin da za su yi wa al’umma ba, ga rayuwa ta yi wa mafi yawan ƴan Nijeriya tsanani saboda gazawar su.” Ya bayyana.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu Da Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari

Tambuwal wanda shi ne shugaban masu neman a zaɓi Atiku Abubakar, ɗan takarar Shugabancin ƙasa a zaɓen 2023, ya buƙaci abokan adawa da su haɗa hannu da ƙarfe domin tabbatar da faɗuwar APC a zaɓe na gaba.

“Hakkin mu ne mu tabbatar APC ta fadi kasa warwas a dukkanin matakan gwamnati.”

Tsohon Gwamnan ya yabawa shugabannin jam’iyyar kan ƙoƙarin da suke yi na riƙe jam’iyyar da manbobin.

People are also reading