Shehu Sani Ya Fadawa Tinubu Ido da Ido Kan Kuskuren da Ya Yi a Hada Kan ’Yan Kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Sanata Shehu Sani ya magantu kan yadda Bola Tinubu zai a hada kan Najeriya cikin sauki a halin da ake ciki.
Sani ya ce taken Najeriya kadai ba zai taba hada kan 'yan kasar ba duba da yadda lamura suka lalace.
Shehu Sani ya ce 'yanci da adalci da kuma daidaito sune kadai za su hada kan 'yan kasar cikin sauki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan ya bayyana haka ne a faifan bidiyo yayin liyafar cin abinci domin bikin dimukradiyya a Abuja a jiya Laraba 12 ga watan Yuni.
"Mai girma shugaban kasa, ina son amfani da wannan dama domin jan hankalinka kan wannan lamari, taken Najeriya ba shi ne zai hada kan Najeriya ba."
"Taken Najeriya ko kundin tsarin mulki ba za su kawo hadin kai ba sai dai adalci da daidaito da kuma samar da 'yanci a kasa."
"Dimukradiyya ba kyauta ba ce daga sojoji kuma ba a caca muka yi nasara ba sai dai jajircewa da sadaukar da kai na wasu 'yan Najeriya."
- Shehu Sani
Shehu Sani ya ce idan Tinubu ya yi nasara za a yaba masa saboda ya yi gwagwarmaya tun farko a siyasa/
Ya ce amma idan ya gaza za a iya cewa wadanda suka kawo dimukradiyya ba su tsinanawa kasar komai ba.
Wannan na zuwa ne yayin da aka gudanar da bikin dimukradiyya a jiya Laraba 12 ga watan Yuni bayan dawowarta a shekarar 1999.
Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nuna damuwa bayan Bola Tinubu ya zame a taro.
Atiku ya jajntawa shugaban inda ya masa fatan yana lafiya bayan tsautsayin da ya afku da shi a Eagle Square.
Asali: Legit.ng