Gwamnatin Kano Ta Mayar da Martani Kan Ɗaga Tuta a Fadar da Aminu Ado Ke Zaune
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi watsi da kafa tuta a fadar Nassawara, inda Sarki na 15 Aminu Ado Bayero ke zaune.
Gwamnatin ta bayyana kafa tutar a matsayin wani yunƙuri na jawo hankalin jama'a, inda ta jaddada cewa Muhammadu Sanusi II ne sahihin Sarkin Kano.
Tutar dai alama ce ta iko da ke nuna cewa sarki yana nan, yawanci an saba kafa ta da karfe 6 na safe kuma a sauke ta da karfe 6 na yammacin kowace rana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka nan kuma a al'adar masarautar Kano, ba a ɗaga tutar idan sarki ba ya nan ko kuma ya yi tafiya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Sai dai da safiyar ranar Alhamis, aka ga an daga tutar tun da karfe 6 na safe a ƙaramar fadar Nassarawa, lamarin da ya janyo cece-kuce a cikin da wajen Kano.
Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II duka suna da’awar sarautar Kano kuma kowanen su na kokarin gudanar da ayyukan masarauta kamar yadda aka saba.
Tun farko dai gwamnatin Kano ta tuɓe Aminu Bayero da sauran sarakuna huɗu, kana ta maido da Sanusi II bayan garambawul da majalisar dokoki ta yiwa dokar masarauta.
Mai magana da yawun gwamna, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya yi fataki da matakin fadar Nassarawa na ɗaga tunar, ya ce wani yunkuri ne na jan hankalin jama'a.
Daily Trust ta ruwaito Sanusi na cewa:
"Wani yunƙuri ne mara amfani na jawo hankalin al'umma, babu wani ruɗani ko shakka kan cewa Sarki Sanusi II shi ne halastaccen Sarkin Kano."
Kuna da labarin Jam'iyyar NNPP ta dage kan cewa har yanzu Muhammadu Sanusi II ne halastaccen sarkin Kano duk da hukuncin kotun tarayya.
Kakakin NNPP, Ladipo Johnson ya ce babbar kotun tarayya ba ta da hurumin sauraron shari'ar saboda sarauta alfarma ce ba 'yanci ba.
Asali: Legit.ng