Home Back

Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi ma’aikata masu fallasa takardun bayanan sirrin gwamnati

premiumtimesng.com 2024/4/27
Gwamnatin Najeriya ta gargaɗi ma’aikata masu fallasa takardun bayanan sirrin gwamnati

Gwamnatin Tarayya ta bayyana wani shiri da ta ke yi domin daƙile fitar kwafe-kwafen bayanan sirrin gwamnati, bayan fitar wasu kwafen bayanai masu nuna irin yadda gwamnatin ke dagargazar kuɗaɗen talakawa, yayin da ake fama da raɗaɗin tsadar rayuwa, ƙuncin rayuwa da tsadar kayan abinci.

Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Folashade Yemi-Esan, ta bayyana damuwar ta dangane da irin yawan fallasa takardun bayanan sirri na gwamnatin tarayya da ake fallasawa ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnatin tarayya.

Cikin wata takardar gargaɗi ta aka raba a ranar 19 ga Fabrairu, wadda sai a ranar Laraba ɗin nan ta faɗo hannun PREMIUM TIMES, Yemi Esan ta ce “gwamnati ta damu ƙwarai da yadda masu yawan fallasa kwafen takardun bayanan sirrin gwamnati.

Ta ce abin ya na sa gwamnati jin kunya da kuma rage mata karsashi a idon jama’a.”

Daga nan ta sha alwashin ladaftar da duk wani ma’aikacin gwamnatin tarayya da aka kama da hannu wajen fallasa sirrin gwamnati.

Cikin takardar sanarwa da gargaɗin wadda aka raba wa a manyan ma’aikatu ciki har da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, Magatakardan Majalisar Ƙasa, Rajistara na Kotun Ƙoli, an umarci kowane babban sakatare da ya gaggauta komawa tsari na isar da saƙon bayanai na zamani, ta hanyar amfani da na’urar sadarwa, domin tabbatar da biyan buƙatar isar da saƙo da kuma killace bayanai.

An dai raba wannan takardar ɗaukar mataki da kuma gargaɗi ne bayan fallasa yadda dakatacciyar Ministar Agaji da Jinƙai, Betta Edu ta bayar da umarnin a saka Naira miliyan 585.2 cikin asusun bankin wata ma’aikaciyar gwamnatin tarayya, lamarin da haramcin sa ya sa aka dakatar da ita, bayan fallasa harƙallar.

Ba dai wannan ne karo na farko da aka taɓa fallasa kwafen bayanan takardun sirri na gwamnatin tarayya ba, waɗanda akasari ɗauke suke da harƙallar maƙudan kuɗaɗe.

 
People are also reading