Home Back

Shugaba Tinubu Ya Bayyana Wani Muhimmin Tagomashi da Gwamnatinsa Ta Samu

legit.ng 2024/6/28
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta ceto ƙasar nan daga mawuyacin halin da ta samu a kanta a ciki a baya
  • Shugaba Tinubu ya ce ya dakatar da halin ƙaƙanikay da Najeriya ta shiga a baya inda yanzu lokaci ne na samun ci gaba
  • Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a fadarsa da ke birnin tarayyya Abuja lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu shugabannin Yarbawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ce watanni 12 na gwamnatinsa abin a yaba ne duk da wasu ƙalubalen da aka fuskanta.

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga tawagar shugabannin ƙungiyar Yarbawa a fadar gwamnati da ke Abuja.

Tinubu ya yi magana kan ceto Najeriya
Tinubu ya ce Najeriya ta fita daga halin kakanikayi Hoto: @DOlusegun Asali: Facebook

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya kamata domin talakawan Najeriya su samu shugabanci mai kyau, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tinubu ya ce kan Najeriya?

Shugaban ƙasan ya ƙara da cewa yanzu ƙasar nan ta tsira daga mawuyacin halin da ta tsinci kanta a baya, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Ya kasance abu mai ƙalubale. Mun karɓi mulki kuma mun dakatar da mawuyacin halin da ƙasar nan ke ciki. Zan iya cewa gaba ɗaya yanzu Najeriya ta fita daga halin ƙaƙanikayi."
"Wannan shi ne alƙawarin da na yi muku, sannan shi ne aikin da kuka ce na yi. Muna yin iyakar bakin ƙoƙarinmu domin ganin mun kai ga tudun mun tsira."
"Abubuwan akwai wahala, ina yin taka tsan-tsan. Lokaci mafi muni ga ƙasar nan ya riga da ya wuce. Za mu yi nasara."
"Ina godiya ga tawaga ta saboda aikin da take yi tuƙuru. Abin da zan yi alƙawari a kai shi ne za mu yi duk abin da ya kamata. Muna da jajircewa sannan za mu yi aiki ta yadda dukkanin ƴan Najeriya za su ji daɗin shugabanci mai kyau."

- Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Tinubu ya yi sabon naɗi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin ACM Shehu Mohammed a matsayin shugaban hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC).

Hakan na ƙunshe ne a cikin takardar naɗin mai ɗauke da kwanan watan 20 ga watan Mayu wacce sakataren gwamnatin tarayya, George Akume ya rattaɓawa hannu.

Asali: Legit.ng

People are also reading