Home Back

Ko kun san sirrin samun nasara a harkar noma?

bbc.com 2 days ago

Ko kun san sirrin samun nasara a harkar noma?

Minti 1 da ta wuce

Wani matashi mai harkar noman kasuwanci, Aminu Murtala Nyako ya ce inganta samar da lantarki a Najeriya zai taimaka sosai wajen bankaɗo ɗumbin albarkar da ke ƙunshe a ɓangaren noma da kiwo.

Aminu Murtala Nyako ya ce lantarki na da matuƙar muhimmanci wajen bunƙasa noma da rage asarar da manoma ke tafkawa bayan sun yi girbi.

Ya ce kamfaninsu na Sabore da ke Adamawa yana hulɗa da makiyaya kimanin 18,000 da ke samar masa da madarar da yake sarrafawa don yin yogot da bota da man shanu da kuma askirin.

A cewarsa, kamfanin yana ƙoƙarin janyo hankalin musamman matasa kan ɗumbin albarka da arziƙin da Allah ya hore wa Najeriya a ɓangaren noma.

People are also reading