Home Back

Dalilin da Ya Sa Muka Gayyaci Nasiru El-Rufai Zuwa Borno Inji Gwamnatin Zulum

legit.ng 2024/5/19
  • Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da gayyatar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai
  • Mai bawa gwamnan shawara ce, Fatima Muhammad Abbas, ta bayyana dalilan gayyatar tsohon gwamnan Kadunan a shafinta na X.
  • A wurin taron, Malam Nasiru El-Rufai ya yi wasu jawabai masu kama da martani wa magajinsa, Sanata Uba Sani.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ziyarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya kai jihar Borno ta jawo ka-ce-na-ce.

Hakan ya biyo bayan ziyarce-ziyarcen da ya kai ne ga wasu 'yan jam'iyyar adawa wanda har hakan ya kai ga hasashen cewa yana shirin chanja sheƙa.

El-Rufai
El-Rufai ya kai ziyarar ne jihar Borno lokacin da ake rade-radin zai sauya sheka. Hoto: MuyiwaAdeyeke Asali: Twitter

Amma ana ta bangaren, wamnatin jihar Borno ta bayyana dalilai da yasa ta gayyaci tsohon gwamnan jihar Kadunan, wanda ta bayyana cewa ziyarar bata da alaka da siyasa

Dalilin gayyatar El-Rufai Borno

Mai bawa gwamnan shawara ce, Fatima Muhammad Abbas, ta bayyana dalilan a shafinta na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta bayyana cewa gwamnatin ne da kanta ta gayyacesa domin ya gabatar da takarda a wurin horo na musamman wa ma'aikata a kan kwarewa wurin zartar da aikace-aikacen gwamnati.

El-Rufai ya yi martani wa Uba Sani

A kwanakin baya dai gwamna Uba Sani ya zargi El-Rufai da barin tarin bashi a jihar Kaduna, wanda hakan ke kokarin hana ayyukan raya kasa a fadin jihar.

Tsohon gwamnan jihar Kadunan ya yi wani zance mai kama da martani wa magajin nasa, Uba Sani, a wurin taron. Ga abinda ya ce kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito:

"Ba na son zama ubangida, shi ya sa ba na tsoma baki a cikin abin da ke faruwa a Kaduna, ina son shi (gwamnan) ya koyi aikin da kansa."
"Ya kamata shugaba ya samu mutanen kirki da za suyi aiki tare. Allah ne kadai zai iya yin komai shi kadai, komi nagartar ka a matsayinka na shugaba, za ka zama ne kamar mutanen da ke kusa da kai, shi ya sa ake cewa gwargwadon nagartar ma'aikatan gwamnatin ku, gwargwadon yadda za ku cigaba.”

El-Rufai ya ziyarci sanatan PDP

A wani rahoton kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya kai ziyara gidan Sanata Abdul Ningi, wanda majalisar dattawa ta dakatar kwanan nan.

Majalisa ta dakatar da Sanata Ningi, mamban jam'iyyar PDP mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya saboda zargin cushe a kasafin kuɗin 2024

Asali: Legit.ng

People are also reading