Home Back

Me ya sa wasu iyaye ke 'matsa' wa ƴaƴansu?

bbc.com 2024/7/5
Worried woman talking on mobile phone at home

Asalin hoton, Getty Images

  • Marubuci, Suneth Perera
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

"Iyayena sun jefa ni cikin damuwa - Nakan sharɓi kuka a kusan kowace rana. Don haka na zaɓi raba gari da su''

Ba kasafai ake jin irin wannan maganganu daga 'ya ba, musamman a yanzu da ita ma ta zama uwa.

Amma Sarika ta ce ta ɗauki matakin ƙaurace wa iyayenta bayan shafe shekaru tana fuskantar ''matsawa'' daga gare su, lamarin da ta ce ya yi tasiri a lafiyar ƙwaƙwalwarta.

"Abin ya shafi lafiyata, musamman a lokacin da na samu juna-biyu. Na tabbata har ɗan da ke cikina zai iya jin kukana a lokacin,'' kamar yadda matashiyar mai shekara 30 ta shaida wa BBC.

Sarika ta sha taiƙata mu'amala da iyayenta, amma matakin da ta ɗauka na nesanta kanta daga iyayen nata ba abu ne mai sauƙi ba.

"Laifina ba zai taɓa gushewa ba," in ji ta.

Sarika ta zauna cikin kaɗaici.

"Zan iya bayyana mahaifina a matsayin mutum mai tsanani. Ba ya zuwa kowace irin harka da ta shafi karatuna a makarantarmu. Hatta bikin kammala karatuna ma bai je ba. Koyaushe sai ya yi ta ba da uzuri," in ji Ashley daga Kenya.

Matashiyar mai shekara 25, ta ce baya ga rashin halartar mahaifinta abubuwan da suka shafeta a makarantar, koyaushe yana ƙorafi game da ita.

"Mahaifiyata ce kawai ta taimakeni daga matsin da na fuskanta a wajen mahaifina. Saboda a koyaushe tana ƙoƙarin daɗaɗa mini,'' kamar yadda ta shaida wa BBC.

"Aurensu ya mutu tsawon lokaci da ya gabata, don haka mahaifiyata ta ci gaba da kula da ni. Saboda rabuwar aure a mafi yawan al'adun ƙasashen Afirka ya bambanta da na ƙasashen Yamma'', in ji ta.

"A yanzu yakan yawan kiran waya domin ya ji ko na samu aiki, don na saya masa abubuwan buƙata."

Asalin hoton, Getty Images

Frustrated pensive teenage African girl sitting on couch at home, looking away, thinking over heartbreak problems, offence, feeling bored, suffering from depression.
Bayanan hoto, "Iyaye masu matsawa" na iya yin tasiri har zuwa lokacin girman yara, in ji masana

Ashley da Sarika na zaune a wurare mabambanta, amma labarinsu ya kusa zuwa ɗaya.

Dukansu sun ce iyayensu sun guje su a lokacin da suke tsaka da buƙatarsu, amma a yanzu suna ƙoƙarin juya su tare da yi musu katsalandan a rayuwarsu da ayyukansu har ma da aurensu.

Wasu da dama sun wallafa bidiyoyi a shafukan TikTok da sauran shafukan sada zumunta, suna bayyana yadda suka guje wa iyayensu sakamakon abin da suka kira ''matsawar iyayen'', wanda ya haifar musu da fargaba da tsoro ba tun suna ƙanana.

"Adadin mutanen - da ke neman agajin ƙwararru kan illar da matsawar iyaye ke haifar musu - na ci gaba da ƙaruwa'', in ji Ayo Adesioye, wata ƙwararriya da ke aiki da ƙungiyar masu kula da mutane da ke fama da lalurorin da suka shafi ƙwaƙwalwa ta Birtaniya.

Me ake nufi da iyaye ‘masu matsawa’?

Asusun Kula da Ƙananan Yara na Unicef, ya ce zama ''iyaye na-gari'' ba bin wata hanya ba ce ko wasu dokoki, ko wani tsari, tsari ne na hanyar rayuwa.

''Ya kamata a yi wa yara tarbiyya ta hanyar mutuntuwa, da martaba su, ba tare da sanya musu fargaba ko nuna ƙyama ba, da taimaka musu ta hanyar nuna musu soyayya da ƙarfafa gwiwa'', in ji Unicef.

Abin da ake nufi da 'iyaye masu matsawa'' shi ne iyayen da ke mu'amalantar yaransu saɓanin wancan abinda Unicef ta bayyana na zama 'iyaye na gari''.

Alal misali ta ce yi wa yaranku tambayar cewa suna da samari ka iya zama matsala. Idan an yi tambayar ta hanyar cin zarafi, to takan iya yiwa yarinya tasiri a rayuwarta.

"A wasu lokuta iyaye kan yi irin waɗanan tambayoyi, ba tare da la'akri da irin illar da haka ka iya yi wa yaran ba, watakila iyayen kan yi hakan ne saboda rashin sanin abin da hakan ka iya haifarwa," in ji Misis Adesioye, wadda ƙwararriya ce a fannnin cin zarafi a gida.

A shekarar 2013, wani bincike ya gano cewa yawan matsin da yara ke sha a lokutan da suek ƙanana ka iya zame musu barazanar kamuwa da wasu cutuka irinsu hwan jini da ciwon siga idan sun girma.

Iyaye masu matsawa da nuna son kai

Misis Adesioye ta yi bayani kan nau'ikan iyaye biyu masu matsawa yaransu da ta sha ganin illolinsu a asibiti.

Na farko su ne iyaye masu ƙoƙarin katsalandan a harkokin 'ya'yansu, musamman fannin karatunsu da abin da suke son zama da inda za su yi aiki, ko da wanda za su yi soyayya, ta hanyar saita musu wasu muradun da ba za a iya cimma su ba.

Sannan akwai wasu iyaye masu nuna son kansu fiye da na yaran, su waɗanan iyaye muradinsu shi ne kan gaba a kan na 'ya'yansu.

Haka kuma kawai wasu nau'ikan iyaye masu raunin tarbiyya, kamar yadda Alyson Corner, wani ƙwararriya kan lafiyar ƙwaƙwalwa a Birtaniya.

Asalin hoton, Getty Images

Asian boy kid sitting and crying on bed while parents having fighting or quarrel conflict at home. Child covering face and eyes with hands do not want to see the violence.
Bayanan hoto, Masana sun ce iyaye da dama kan jefa 'ya'yansu cikin damuwa, musamman a lokutan rabuwar aure da rayuwar aurensu.

Bayan ta ajiye aiki daga hukumar Lafiyar Birtaniya, Misis Corner ta ƙaddamar da wani shafi, domin wallafa dabarun da za su taimaka wa matasan da suka fuskanci rayuwa ƙarƙashin matsawar iyaye, domin taimaka musu manta abubuwan da suka faru, don su ci gaba da rayuwarsu

Ta wasu daga cikin nau'o'in iyaye masu matsawa sun haɗa da:

  • Iyaye masu nuna ƙarfin iko - Su ne waɗanda ke ɗukar matakai kan 'ya'yansu ba tare da jin ta bakinsu.
  • Iyaye marasa haƙuri - Su ne waɗanda suke fusata kan duk laifin 'ya'yansu suka aikata.
  • Iyaye masu ci ga gumin 'ya'yansu - Su ne iyayen da ba su iya ɗakar nauyin kansu, suke kuma dogaro a kan abin da 'ya'yansu suka mallaka.
  • Iyaye masu kishi da 'ya'yansu - Su ne iyayen da suke yin kishi da abin da 'ya'yansu ke yi ko suke sukarsu idan sun yi wani abin a yaba
  • Iyaye masu saurin fushi - Su ne iyayen da ke saurin fushi a kan ƙanƙanin abu.
  • Iyayen da ke bar wa uwaye ɗawainiyar 'ya'yansu - su ne iyaye mazan da ke barin komai da ya jiɓanci 'ya'yansu a hannun matayensu.

Asalin hoton, Getty Images

In this photo illustration the logo of US online social media and social networking site 'X' (formerly known as Twitter) is displayed centrally on a smartphone screen alongside that of Threads (L) and Instagram (R).
Bayanan hoto, Mutane da dama sun wallafa bidiyon yadda suka guje wa iyayensu masu matsawa

Abin da al'ada ke ƙyama

Sarika ta ce "A al'adarmu mukan ɗauka cewa koyaushe iyaye ne a kan daidai, yara ne ke yin kuskure. ''Masu iya magana kan ce ruwa ba ya tsami banza'', in ji ta.

Farfesa Cheris Shun-ching Chan, ƙwararriya kan ilimin zamanatakewar ɗan-adam a jami'ar Hong Kong ta ce akwai wasu dalilai na rayuwa da tattalin arziki da ke haddasa batun.

Ta ce alal misali tsarin rayuwar haihuwar ɗa-ɗaya a China, wanda ya taƙaita wa iyaye samun haihuwa, zai sanya wa yara matsi, saboda iyayen ba su da wasu 'ya'yan da za su dogara da su.

"Kuma waɗannan yaran na cikin tsananin matsin lamba domin cika muradin iyayensu, saboda iyayen nasu sun sadaukar da komai domin cimma muradunsu,'' kamar yadda ta shaida wa BBC.

Farfesa Chan ta ce a wasu lokuta, iyaye da dama kan dogara da 'ya'yansu, waɗanda suka sha cuzguna musu, musamman idan aka samu rabuwar aure tsakanin iyayen, ko kuma idan mahaifin na da wata matar daban.

Asalin hoton, Getty Images

A silhouette of a happy young girl child the arms of his loving mother for a hug, in front of the sunset in the sky on a summer day.
Bayanan hoto, "Bana son in zama kamar iyayena, Ina son tallafa wa 'yata''.

Ayo Adesioye, ta ce wasu daga cikin tasirin illolin da iyaye masu matsawa ke yi wa 'ya'yansu har zuwa girma sun haɗa da yaro ya zama shiru-shiru, mai tsananin jin kunya da rashin yarda da kai da kuma da tsananin buƙatar taimako da rashin iya neman taimako da kuma rashin jin nutsuwa a soyayya.

Yadda za ka rayu da iyaye masu matsawa

Sarika ta ce mu'amala da iyayenta ta kasance mai tsananin wahala, bayan aurenta, wanda iyayen nata ba su aminta da shi ba.

"Iyayena sun riƙa nuna min abubuwa a fili. Babu abin da na yi musu, amma kullum mahaifina sai kalmomi marasa daɗi yake furta mini.''ke dai Allah wadaranki'', abin da kullum yake gaya mini kenan, a wasu lokuta nakan yi tunanin cewa ni bani da wata ƙima.

''Babu wanda yake kula da lafiyar ƙwaƙwalwata,'' in ji ta.

Ayo Adesioye ya ce ba tare da yin jayayya da iyaye ba, ya kamata 'ya'ya su da suka fara manyata su yi wa kansu iyaka, dangane da batun da ya kamata su riƙ tattaunawa da iyayensu, tare da yarda cewa su ba yara ba ne.

"Ina ganin abin da ake kewar kenan. Na ga wannan da yawa a cikin al'amurana. Ka ɗauka cewa kai yaro ne, ka manta da cewa kai babba ne."

Ashley ta bi wannan shawarar kuma ta zaɓi ta kafa matsakaitan iyakoki tare da mahaifinta, da kuma fifita lafiyar tunaninta, yayin da Sarika a yanzu ta ƙudurta zama uwa tagari ga ɗiyar da ta haifa.

"Ba na so in zama kamar iyayena, ina so in taimaka mata sosai, in ba ta mafi kyawun abin da za ta yi, kuma in bar ta ta yanke shawarar rayuwarta," in ji ta.

People are also reading