Home Back

Shigar malamai siyasa zai ruguza dimokraɗiyyar Najeriya - Buba Galadima

bbc.com 2024/7/5

Shigar malamai siyasa zai ruguza dimokraɗiyyar Najeriya - Buba Galadima

Mintuna 7 da suka wuce

Wani babban ɗan adawa a Najeriya, ya ce shigar malamai ko shugabannin addinai cikin harkar siyasa dumu-dumu, abu ne mai hatsarin da zai iya ruguza dimokraɗiyyar ƙasar.

Shigar malamai cikin harkokin siyasa, batu ne mai matuƙar haddasa ka-ce-na-ce a Najeriya.

A cewar Buba Galadima, shigar malamai dumu-dumu cikin siyasa na ɗaya daga cikin koma-bayan da dimokraɗiyyar Najeriya ta samu a cikin shekara 25.

Yana jawabin ne a wani ɓangare na hirarrakin da BBC ta yi da wasu ƙusoshin siyasa kan cika shekara 25 na mulkin farar hula ba tare da katsewa ba a Najeriya.

Ya ce ɗaukan ɓangare cikin harkokin siyasa ga shugabannin addinai, yana nema ya yi ƙarfi kuma zai iya ruguza mulkin dimokraɗiyyar Najeriya.

Jigon na jam'iyyar NNPP ya ce malamai waɗanda ake yi wa kallon iyayen al'umma, bai kamata su riƙa cin alwashi a kan duk wani ɗan siyasa ba.

People are also reading