Talakawa basu cin kawai saboda haka ba za mu saka cikin abincin da gwamnati za ta rage kudin su ba – Eno
Gwamnan jihar Akwa-Ibom Umo Eno ya ce ba zai saka kwai a cikin jerin kayan abincin da zai rage farashin su a jihar ba.
Eno ya fadi haka ne da yake Saka hannu a takardar dokar rage farashin abinci a jihar da kwamitin zantaswa ta jihar ta yi ranar Alhamis.
Eno a makonnin da suka gabata ya mika wa majalisar dokokin jihar, kudirin kafa hukumar siyar da kayan abinci da na masarufi a jihar domin siya da siyar wa talakawa cikin farashi mai rahusa.
Bisa ga dokar gwamnati za ta siya kayan abinci kamar shinkafa, wake da garin kwaki ta siyar wa mutane a farashi mai sauki.
Gwamnan ya ce “Talakwa basu cin kwai saboda haka bashi cikin abincin da za a rage kudin su don talakawa.