Home Back

Tsohuwar 'Yar Majalisar Wakilai Ta Yi Nasara Yayin da APC Ta Lashe Zaben Ciyamomi a Gombe

legit.ng 2024/5/18
  • Jam'iyyar APC a jihar Gombe ta yi nasara a zaben ƙananan hukumomi 11 da aka gudanar a yau a fadin jihar baki daya
  • Jam'iyyar ta lashe dukkan zabukan da aka gudanar har da na kansiloli a unguwanni 114 a yau Asabar 27 ga watan Afrilu
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da baturen zaben, Sa'idu Awak ya fitar bayan kammala zabe a jihar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Gombe - Jam'iyyar APC ta lashe dukkan zabukan ƙananan hukumomi da kansiloli da aka gudanar a jihar Gombe.

Daga cikin wadanda suka samu nasara kawai tsohuwar mamban Majalisar Tarayya, Fatima Binta Bello.

Jam'iyyar ta lashe dukkan zabukan ƙananan hukumomi 11 da na kansiloli 114 da aka gudanar a yau Asabar 27 ga watan Afrilu, cewar Leadership.

Baturen zaben, Sa'idu Awak shi ya sanar da haka bayan kammala zaben da aka gudanar a jihar inda ya ce APC ta lashe zaben ba tare da hamayya ba.

Awak ya ce a zaben karamar hukumar Gombe, dan takarar jam'iyyar APC, Sani A. Haruna shi ya lashe zaben da kuri'u 72,286.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da mai bi masa a jam'iyyar PDP ya zamo na biyu da kuri'u 1,678 a zaben karamar hukumar.

A kananan hukumomin Kaltungo da Shongom, 'yan takarar jam'iyyar, Iliya Sulaiman Jatali da Fatima Binta Bello sun yi nasarar lashe zaben.

Binta Bello wacce tsohuwar 'yan Majalisar Tarayya ce da ta wakilci yankin mazabar Kaltungo/Shongom ta yi nasara a zaben karamar hukumar Shongom.

Asali: Legit.ng

People are also reading