Home Back

TSADAR ABINCI: Za a raba wa kowane gwamna lodin tirela 60 na takin zamani, sanata tirela 2, ɗan majalisar tarayya tirela 1- Akpabio

premiumtimesng.com 2024/8/24
Gwamnatin Borno ta gargadi mutane kada su rika siyar da abincin tallafi da gwamnati ke raba musu

A ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na farfaɗo da sauƙin tsadar rayuwa, kwanan nan za a raba wa kowane gwamnan jiha lodin tirela 60 na takin zamani, domin raba wa manoma.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya bayyana haka a majalisa a ranar Talata.

Ya ce su ma sanatoci za a bai wa kowa tirela 2 na lodin takin zamani, domin rabawa a mazaɓar sa. Haka su ma mambobin tarayya za a ba kowa lodin tirela ɗaya domin ya kasafta wa manoman mazaɓar sa.

Akpabio ya bayyana haka lokacin da yake maida jawabi kan wani koke da Sanata Sunday Karimi na Jihar Kogi ya yi, wanda ya yi kiran gaggawa ga gwamnatin tarayya ta shawo kan masifar tsadar kayan abinci.

“Za a bai wa kowace jihar lodin tirela 60 na takin zamani, haka su ma sanatoci da mambonin tarayya za a raba masu, domin su ma su raba wa mazaɓun su,” cewar Akpabio.

Sai dai kuma Akpabio ya shaida wa ‘yan jarida cewa kada su ce wannan magana daga bakin sa ta fito. Ya ce a ce shi ma ji ya yi daga bakin Shugaban Kwamitin Harkokin Noma na Majalisar Dattawa, Sanata Saliu Mustapha.

“A to, don kada gobe na yi baƙin jini a wurin gwamnoni, su ce na ari bakin su na ci masu albasa.”

People are also reading