Home Back

Rigimar Sarautar Kano Ta Ƙara Tsananta, Majalisa Ta Garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara

legit.ng 2024/6/29
  • Yayin da taƙaddama kan sarautar Kano ke ƙara ƙamari, majalisar dokokin jihar ta shigar ƙara a gaban kotun ɗaukaka ƙara
  • Majalisar ta buƙaci kotun ɗaukaka kara ta dakatar da shari'ar sarauta da ke gaban babbar kotun tarayya, kana ta dawo da iya gabanta
  • Tuni dai Babban Kotun Tarayya mai zama a Kano ta shirya yanke hukuncu kan halascin tube Sarki na 15, Aminu Ado Bayero da sarakuna hudu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta garzaya kotun ɗaukaka ƙara kan rigimar sarautar da ta ƙi ci kuma ta ƙi cinyewa a jihar.

Majalisar ta roƙi kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da shari'ar da Sarkin Dawaki Babba, Aminu Babba Danagundi ya shigar gaban babban kotun tarayya.

Sarki Sanusi II da Aminu Ado.
Majalisar dokokin jihar Kano ta ɗaukaka kara kan rigimar masarautar Kano Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Imran Muhammad Asali: UGC

Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, Ɗanagundi ya ƙalubalanci sabuwar dokar masarautar Kano, 2024 wanda ta tube sarakuna biyar na jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ƴan majalisar sun buƙaci kotun ɗaukaka ƙara ta dawo da shari'ar hannunta saboda yadda ake samun saɓanin umarni tsakanin babbar kotun jiha da ta tarayya.

Mai shari’a Mohammed Liman na babbar kotun tarayya da ke Kano ya yanke hukuncin cewa kotun tana da hurumin sauraron ƙorafin Sarki na 15, Aminu Ado.

Ya kuma sanya ranar 20 ga watan Yunin da muke ciki domin yanke hukunci kan halascin sabuwar dokar masarauta wadda ta tsige basaraken da sauran sarakuna huɗu.

Bisa rashin gamsuwa da matakin, majalisar dokokin Kano ta hannun lauyanta, Eyitayo Fatogun (SAN) ta shigar da ƙara mai lamba CA/KN/ /26/2024 a kotun ɗaukaka ƙara.

Lauyan ya roƙi kotun ɗaukaka ƙara ta dakatar da Ɗanagundi a yunƙurinsa na soke sabuwar dokar masarautar Kano da dawo da tsohuwar dokar da majalisar ta warware.

Ya buƙaci kotun ɗaukaka ƙarar ta dakatar da shari'ar da ke gaban babbar kotun tarayya na wucin gadi har sai ta yanke hukunci kan ƙarar da majalisa ta ɗaukaka.

Waɗanda ake tuhuma a ƙarar sun haɗa da Alhaji Ɗanagundi, gwamnatin Kano, Antoni Janar na Kano, sufetan ƴan sanda, kwamishinan ƴan sanda, hukumar NSCDC da DSS.

Kwankwaso ya fallasa maƙiyan Kano

A wani rahoton kun ji cewa jagoran NNPP na ƙasa ya bayyana yadda ƴan Kwankwasiyya suka sha fama da maƙiyan siyasa tun zaɓen 2019 har zuwa yanzu

Rabiu Kwankwaso ya ce ga dukkan alamu waɗannan maƙiyan sun sake dawowa su wargaza Kano a rikicin sarautar da ke faruwa.

Asali: Legit.ng

People are also reading