Home Back

Za a yi gwanjon uku daga cikin jiragen shugaban kasa

premiumtimesng.com 2024/7/1
Za a yi gwanjon uku daga cikin jiragen shugaban kasa

Gwamnatin tarayya za ta yi gwanjon wasu jirage uku daga cikin jiragen shugaban kasa saboda tsufa da suka yi da kashe kuɗaden kula da su da ake yi.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro da leken asiri na kasa ya ba da shawarar cewa a sayi sabbin jirage biyu na shugaban kasa da mataimakinsa saboda tsufa da waɗanda suke amfani da shi ya yi.

Shehu Buba Umar, shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin tsaro da leken asiri, shi ma ya goyi bayan shawarar da kwamitin majalisar ya bayar.

Siyar da jiragen guda uku zai rage adadin jiragen saman shugaban kasa zuwa uku.

Yanzu akwai jirage guda shida sannan da jirage masu saukar angulu guda huɗu da shugaban kasa da mataimakin sa ke amfani da su.

Yanzu dai jiragen da sashen kula da jiragen saman shugaban kasa da ke karkashin ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, sun haɗa da
Boeing 737 Boeing Business Jet (BBJ), Gulfstream G550, Gulfstream GV, Falcon 7x guda biyu da Challenger CL605 guda ɗaya.

Majiya ta shaida cewa kusan rabin jiragen saman sun tsufa sannan suna bukatar gyare-gyare kusan kullun da hakan ya sa suka kawai wahala da kashe kuɗaɗe za arika yi musu ba tare da sun biya buƙata yadda ake so ba.

Hakan ya sa rabuwa da su shine mafita da sauki idan ana son zaman lafiya batare da ana ɓarnata kuɗi ba sannan kuma a kare ba a samu yadda ake so ba.

Jiragen uku da aka za a yi gwanjon su sun haɗa da Boeing 737 Boeing Business Jet (BBJ), da Gulfstream ɗaya da kuma Falcon 7x.

Tuni dai har gwamnatin tarayya ta ba wa kamfanin JetH na kasar Amurka kwantieagin ƴan dillancin jiragen.

People are also reading