Home Back

Gwamnan Kano ya sake naɗa Ogan ɓoye muƙami da wasu mutane takwas

dalafmkano.com 2024/5/18

A ƙoƙarin sa na ci gaba da kawo cigaba a jihar sa Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya sake naɗa Ambasada Yusuf Imam Ogan Ɓoye, a matsayin mai bashi shawara a kan harkokin matasa da wasanni, tare da naɗa wasu mutane takwas waɗanda za su taimaka masa a fannoni daban-daban.

Babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin, ya ce Gwamnan ya amince da naɗa mutanen ne kamar haka;

An naɗa Farfesa Ibrahim Magaji Barde, a matsayin mai bai wa gwamnan shawara na musamman a kan harkokin tattara kuɗaɗen shiga (IGR).

Sai kuma Dr. Abdulhamid Danladi, da aka naɗa shi a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin kasashen waje na II.

An kuma naɗa Engr. Bello Muhammad Kiru, mai bashi shawara na musamman kan albarkatun ruwa.

Yayin da aka sake naɗa Ambasada Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) a matsayin mai bai wa gwamna shawara na musamman a kan harkokin matasa da wasanni a jihar.

Har ila yau, Dr. Nura Jafar Shanono, shi kuma an ɗauke shi daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Darakta, a ma’aikatar Ruwa da Gine-gine (WRECA) ta jihar Kano.

Shi kuwa Baba Abubakar Umar, ya samu sauyi daga mai bai wa gwamna Kano shawara na musamman ga harkokin makarantu masu zaman kansu, zuwa ma’aikatar dake kula da ma’aikatan wucin gadi.

An kuma nada Hon. Nasir Mansur Muhammad, a matsayin shugaban hukumar , ƙanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEs).

Yayin da Aminu Hamidu Bako Kofar Na’isa ya zama mataimakin shugaban Hukumar kula da Albarkatun Noma da Raya Karkara ta Kano (KNARDA).

Shi kuwa Engr. Mukhtar Yusuf, an naɗa shi a matsayin mataimakin shugaban hukumar kula Albakatun ruwa Ruwa da Gine Gine (WRECA).

Sanusi Bature ya kuma ce, naɗin ya fara aiki ne nan take, inda Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kuma taya su murna tare da fatan alkhairi.

People are also reading