Home Back

Kwango: Kotu ta yanke wa sojoji 25 hukuncin kisa

dw.com 3 days ago
Demokratische Republik Kongo Gericht Symbolbild
Hoto: Pond5/IMAGO

A jimilce dai mutane 31 ne da suka hadar da mata fararen hula guda hudu da sojoji 27 aka gufarnar a yayin zaman wuni guda da kotun hukunta sojoji ta Butembo mai mazauni a arewacin Kivu ta yi a ranar Laraba 03.07.2024.

Guda daga cikin lauyoyin da ke kare wadanda ake tuhuma Barista Jules Muvweko ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP aniyarsu ta daukaka kara kan hukunci kisan da ya shafi kyaftin biyu, duk da cewa an wanke sauran daga laifin saboda rashin cikakkun hujjoji.

Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan tawayen M23 masu samun goyon bayan Ruwanda ke matsa lamba, lamarin da ya kai su ga karbe iko da yankuna da dama na arewacin Kwango.

People are also reading