Home Back

Ana zargin wani matashi da kashe kannensa mata biyu da Muciya a Kano

dalafmkano.com 2024/5/13

An shiga ruɗani yayin da aka yi zargin wani matashi da kashe ƙannensa mata su biyu a unguwar Hausawar Mandawari da ke jihar Kano.

Tuna fari dai matashin ana zargin ya hallaka ƙannen nasa ne ta hanyar dukansu da muciya wanda har sai da rai ya yi halinsa, a dai-dai lokacin da iyayen su basa gida.

Wata mata da ta kasance maƙociyar gidan da lamarin ya faru ta ce, bayan faruwar lamarin ne matashin ya fito riƙe da muciya yana faɗin cewar yara biyun duk ya kashe ƙannen nasa da suke iyaye ɗaya guda biyu, sai dai ta ce matashin yana da lalurar taɓin Aljanu kamar yadda iyayen sa suka sanar musu.

A cewar wata matashiya da ta ganewa idanun ta faruwar lamarin ta ce, suna suna gida suka tarar da gawar yaran su biyu ɗauke da jini a jikin su, inda matashin ya shaida musu cewar shine ya kashe yaran biyu.

Alhaji Lawan Bala Umar shi ne mai unguwar Hausawa, ya ce bayan faruwar al’amarin ne suka sanar da jami’an tsaro mafi kusa, domin ɗaukar mataki na gaba.

Ya ƙara da cewa, yaran da aka kashe akwai ƴar shekara hudu, da kuma wacce bata wuce shekara biyu da rabi ba.

Wakiliyarmu Madina Shehu Hausawa ta rawaito cewa, tuni dai jami’an tsaro suka dauke gawarwakin yaran don kai su asibiti a wani mataki na fara bincike kan lamarin.

Sai a biyo mu a labaran mu na gaba don jin martanin rundunar yan sanda a kan wannan al’amari.

People are also reading