Home Back

‘Yan Fashin Daji Sun Sace Wasu ‘Yan Jarida Da Mata Da Wasu Yara 2 A Kaduna

leadership.ng 2024/10/6
‘Yan Fashin Daji Sun Sace Wasu ‘Yan Jarida Da Mata Da Wasu Yara 2 A Kaduna

Wasu gungun ‘yan bindiga a ranar Asabar, sun kutsa kai yankin Danhonu da ke cikin Millennium na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna, inda suka yi awon gaba da wasu ‘yan jarida biyu na jaridar The Nation da Blueprint.

‘Yan jaridar sun haɗa da Alhaji AbdulGafar Alabelewe da AbdulRaheem Aodu, tare da matansu da ‘ya’yansu.

Wakilin LEADERSHIP ya ruwaito cewa, Alhaji Alabelewe shi ne shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) a majalisar jihar Kaduna a halin yanzu.

Wani daga cikin ‘yan uwan ɗaya daga cikin waɗanda abub ya shafa, Taofeeq Olayemi, ya tabbatar da faruwar kai harin, ya ce ‘yan bindigar sun je yankin da misalin karfe 10:30 na daren ranar Asabar, inda suka yi ta harbe-harbe ba ƙaƙƙautawa kafin su yi awon-gaba da su.

Taofeeq ya ce ‘yan fashin mutanen sun yi garkuwa da Alhaji Alabelewe da matarsa ​​da ’ya’yansa biyu, sai kuma Alhaji Aodu da matarsa, inda suka bar ‘yarsu da ba ta da lafiya ba su ɗauke ta ba.

“Da farko sun ɗauki Alhaji Abdulgafar da matarsa ​​da ‘ya’yansa uku da wata yarinya suka zauna tare da su kafin su nemi yarinyar ta dawo da daya daga cikin yaran, sai suka tafi da Abdulgafar da matarsa ​​da ‘ya’yansa biyu.

“Sun farfasa musu kofofin gida da tare da lalata mudu gida da yi musu ɓarna bayan sun shiga ciki,” inji shi.

Da aka tuntuɓi Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, ASP Mansir Hassan, an kasa samun wayarsa har zuwa lokacin da muke haɗa wannan rahoton.

People are also reading