Home Back

Kano: Bidiyon Kwamandojin Hisbah 44 a Fadar Sarki Sanusi II, Sun Fadi Matsaya

legit.ng 2024/7/2
  • Shugabannin Hisbah a kananan hukumomi 44 a Kano sun yi mubaya'a ga Sarki Muhammadu Sanusi II a jihar
  • Kwamandojin sun ziyarci sarkin ne a fadarsa jiya Litinin 10 ga watan Yuni domin nuna goyon bayansu
  • Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shari'a bayan mayar da Muhammadu Sanusi II kujerar sarauta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da mubaya'a ga Sarki Muhammadu Sanusi II, Hukumar Hisbah ta ziyarci sarkin a fadarsa.

Shugabannin hukumar a kananan hukumomi 44 da ke jihar sun yi mubaya'a ga Sarki Sanusi II a fadarsa.

Hukumar Hisbah ta ziyarci Sanusi II a Kano
Kwamandojin Hisbah sun kai ziyara fadar Sarki Sanusi II a Kano. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa. Asali: Facebook

Kano: Ziyarar Hisbah fadar Muhammadu Sanusi II

A cikin faifan bidiyo da Kano Emirate Council ta wallafa a shafin X, an gano kwamandojin suna sarawa Sanusi II.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamandojin sun kai ziyarar a jiya Litinin 10 ga watan Yuni a fadar sarkin domin nuna goyon baya.

Daga bisani an gudanar da addu'o'i domin neman taimakon ubangiji kan jagorancin sarkin da ci gaban Kano.

Halin da ake ciki kan shari'ar masarautu

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwar sarautar jihar a kotu bayan tuge sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Babbar kotun jihar ta yi zama kan shari'ar inda ta sanya Alhamis 13 ga watan Yuni domin ci gaba da sauraran karar.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading