Home Back

Sancho na son komawa Dortmund, ƙungiyoyin Saudiyya na zawarcin Alisson

bbc.com 2024/7/6
Jadon Sancho

Asalin hoton, getty images

Ɗan wasan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 24, zai matsa kaimi don komawa Dortmund kan kwantiragi na dindindin daga Manchester United a wannan bazarar. (Star)

Ƙungiyoyin gasar Saudi Pro League sun ayyana golan Liverpool da Brazil Alisson, mai shekara 31 a matsayin ɗaya daga cikin manyan waɗanda za su yi zawarci a wannan bazarar. (Teamtalk)

Aston Villa na shirin kammala cinikin £5m kan ɗan wasan tsakiyar Ingila Ross Barkley, mai shekara 30, daga Luton Town. (talkSPORT)

Arsenal za ta iya barin dan wasan Ingila Eddie Nketiah, mai shekara 25, ya bar kulob ɗin, inda Fulham ta shirya miƙa tayin kusan fam miliyan 30 kan dan wasan wanda kuma ke jan hankalin Crystal Palace da Wolves da Everton. (Sun)

Har ila yau Gunners ɗin na shirin karɓan tayi kan ɗan wasan baya na Ukraine Oleksandr Zinchenko, mai shekara 27, wanda ake alakanta shi da Bayern Munich. (Football Insider)

Manchester United da Liverpool suna sanya ido kan ɗan wasan bayan Sporting Lisbon da Portugal Goncalo Inacio mai shekara 22. (Fabrizio Romano)

Sunderland ta kuduri aniyar ba za ta sayar da matashin ɗan wasan Ingila Jobe Bellingham, mai shekara 18 ba, yayin daTottenham da Brentford da Crystal Palace duk suke zawarcin dan wasan. (Guardian)

Real Madrid ta yanke shawarar yin amfani da damar da take da ita na sayen ɗan wasan gaban Sifaniya Joselu, mai shekara 34, kan cinikin dindindin daga Espanyol. (The Athletic)

AC Milan ta shirya ɗaukar kocin Lille Paulo Fonseca, mai shekara 51, don maye gurbin Stefano Pioli a matsayin kocinta a kakar wasa mai zuwa. (La Gazzetta dello Sport)

Burnley ta tuntubi tsohon kocin West Ham da Newcastle da Crystal Palace Alan Pardew, mai shekara 62, yayin da ta fara neman wanda zai maye gurbin Vincent Kompany. (Sun)

People are also reading