Sarautar Kano: Abba Kabir Ya Magantu Kan Sahihancin Samun Takarda Daga Kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan sahihancin takardar kotu da ke haramta tube sarakuna biyar a jihar.
Gwamnatin ta ce har yanzu ba ta samu wata takarda musamman da ke haramta abin da gwamnan ya aikata ba kan kujerar sarautar jihar.
Kwamishinan shari'a, Barista Haruna Isah Dederi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka yada a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dederi ya ce har zuwa wannan lokaci babu wata takarda da gwamnatin Kano ta samu kan wannan mataki da ake magana.
Ya bayyana cewa shi ne mutum na farko da ya kamata ya samu takardar a matsayinsa na kwamishinan Shari'a amma bai ga komai ba.
"Ina amfani da wannan dama domin fadawa mutanenmu gaskiyar lamari kan takardar da ke yawo a kafafen sadarwa."
"A iya sani na babu wata takarda ta umarnin kotu da aka damkawa gwamnatin Kano kamar yadda ake yadawa."
"Idan har za a ba da wani umarni to dole ta hannuna za a mika a matsayina na kwamishinan shari'a."
- Haruna Dederi
Kwamishinan ya ce a doka kotu bata ba da umarni kan abin da aka riga aka kammala shi inda ya ce har yanzu suna dakon jiran takardar daga kotu.
Ya bukaci al'ummar jihar Kano su kwantar da hankulansu su bar jita-jita kan abin da ake yadawa a kafafen sadarwa da ba a dogara da su ba.
Kun ji cewa, Mallam Nuhu Ribadu ya yi barazanar maka mataimakin gwamnan Kano, Abdulsalam Aminu Gwarzo a gaban kotu kan bata masa suna.
Ribadu ya dauki wannan matakin ne bayan Gwarzo ya zarge shi da hannu a rikicin sarautar jihar Kano.
Asali: Legit.ng