Home Back

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu-Maryam Labarina

leadership.ng 2024/4/29
Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu-Maryam Labarina

Jaruma a masana’antar Kannywood Fatima Hussaini wadda aka fi sani da Maryam Labarina bayan fitowarta a kayataccen shiri mai dogon zango na Labarina da kamfanin Saira Mobies yake shiryawa ta bayyana cewar kamar role din da ta hau a cikin shirin Labarina inda ta dage sai ta auri talakan mutum haka abin yake ko a zahiri.

Fatima wadda ta bayyana nasarori da kalubale da ta fuskanta tun bayan fitowarta a cikin shirin na Labarina,yayin wata hira da tayi da yan jarida,ta tabbatar da cewar muddin wani talaka yazo neman aurenta to zata iya aurensa matukar dai suna son juna kuma sun fahimci junansu,domin kamar yada tace wasu sai sun yi aure Allah yake azurta su yayin da wasu kuma koda sunyi aure da arzikinsu daga baya kuma suke talaucewa.

Ni haifaffiyar garin Jos ta jahar Filato inji Maryam inda nayi karatun Firamare da Sakandire kuma yanzu haka nake aji daya na makarantar gaba da Sakandire ta Nuhu Bamalli Polytechnic da ke Zariya inda nake karatun aikin gwajin Lafiya.

Ta ci gaba da cewa kafin ta fito a shirin Labarina ta fito a wasu fina finai da suka hada da Amarya, Fatake Sirrin Kyau, Na Ladidi da sauransu, amma kuma shirin Labarina da ta fito yasa ta zama abar kwatance ga masu sha’awar kallon fina finan Kannywood duba da matsayin da ta fito a matsayin mace mai gudun Duniya.

Maryam ta kuma yi kira ga wadansu da suke amfani da sunanta suna bude shafuka a kafafen sada zumunta da su dinga  yi mata adalci a duk lokacin da zasu dora wani faifan bidiyo domin su kare mata mutuncinta a lokacin da suke neman abinci.

Daga karshe ta bayyana cewar babban burin da take son cimmawa a halin yanzu bai wuce masana’antar Kannywood ta koma shirya manyan fina finai kamar yadda ake yi a masana’antar Bollywood da Hollywood ta kasar Amurka ba.

 
People are also reading