Kano: Abba Kabir Ya Tura Sunan Ɗan Kwankwaso da Mutum 3 Majalisa Domin Tantancewa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sake tura sunayen mutane hudu Majalisar dokokin jihar domin tantance su.
Abba ya tura sunayen Majalisar ce domin tantance su a matsayin ƙarin kwamishinoni a jihar.
Daga cikin wadanda aka tura akwai ɗan tsohon gwamnan jihar, sanata Rabiu Musa Kwankwaso mai suna Mustapha Kwankwaso.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada da Adamu Aliyu Kibiya da Usman Shehu Aliyu da kuma Abduljabbar Garko.
Daga cikinsu akwai Adamu Aliyu Kibiya wanda shi ne aka dakatar kafin yanke hukuncin zaben jihar saboda katoɓarar da ya yi ga alkalan kotu.
Kibiya ya yi barazanar ce inda ya ke zargin akwai kullalliya cewa an ba alkakan kudi za su yi hukuncin da bai dace ba.
Daga bisani gwamnan jihar ya dakatar da shi bayan korafe-korafe daga jama'a wanda ake ganin barazana ce ga zaman lafiyar jihar.
A kwanakin baya, gwamnan ya ba kwamishinonin wa'adin kwanaki da su rubuto ayyukan da suka yi a ma'aikatunsu domin sanin makomarsu a gwamnati.
Legit Hausa ta ji ta bakin hadimin Gwamna Abba Kabir a bangaren kafar sadarwa ta zamani kan wannan nadi.
Salisu Yahaya Hotoro ya ce babu batun cece-kuce kan wannan saboda ɗan Kwankwaso shi ma ɗan kasa ne kuma ya na da gogewa da zai rike kowane mukami.
"Ɗan Kwankwaso shi ba ɗan jihar Kano ba ne?, shin akwai wata doka da ta ce shi ba zai rike wani mukami ba? Ya yi karatu ya na da gogewa na rike dukkan mukamin da aka ba shi."
"Bayan haka ba yau ya shiga siyasa ba duk kamfe da shi muka yi a kananan hukumomi 44, ya ba da dukkan gudunmawa."
- Salisu Yahaya Hotoro
Hotoro ya ce shi bai ga abin cece-kuce kan wannan lamari ba, ko da kuwa Rabiu Kwankwaso ne ya tura sunansa ai hidimar da ya yi wa jihar Kano da NNPP ya cancanci a ba shi kowace irin kujera.
A baya, mun kawo muku cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kai ɗauki ga wasu ƙauyukan jihar kan rashin ruwan sha.
Ƙauyukan sun hada da Danya da Kyallin Bula wadanda suka dade cikin halin matsin rashin ruwan sha a ƙaramar hukumar Bichi.
Ƙauyukan sun shafe shekaru a wahala sakamakon wuyar da suke sha wajen samun ruwan da za su yi amfani da shi.
Asali: Legit.ng