Home Back

SARƘA UWAR RIKICI: ‘Yan Majalisar Tarayya 60 sun yi barazanar ficewa daga PDP, sun nemi a tsige Damagum, Shugaban Riƙon PDP

premiumtimesng.com 2024/5/7
DAGA WAKILAN JAMA’A:  ‘Yan Majalisa sun manta da matsalar tsaro da ta tsadar rayuwa, sun haƙiƙice kan yi wa ƙungiyoyin kishin jama’a takunkumi

‘Yan Majalisar Tarayya su 60 sun yi barazanar ficewar daga PDP, tare da neman a cire Shugaban Riƙo na PDP na Ƙasa, Bello Damagum.

‘Yan Majalisar sun yi zargin cewa ana ƙulle-ƙullen ƙaƙaba wa PDP wasu jami’an APC a matsayin mambobin riƙon ƙwarya, domin tsara wani ɓoyayyen shirin su.

Sun yi wannan barazanar ce sakamakon rikicin da ya dabaibaye PDP a Jihar Ribas da wasu jihohi 10.

Ɗan Majalisar Tarayya Ikenga Ugochinyere daga Jihar Imo ne shi da wasu mambobi 5 suka gabatar da wannan gargaɗin, a wurin wani taron manema labarai, a Majalisar Tarayya, a Abuja, ranar Litinin.

Sun kuma nemi a cire Shugaban Riƙo na Jam’iyyar PDP, Umar Damagum, kafin taron Majalisar Zartaswar PDP mai zuwa.

Su shida ɗin sun ce su na magana ne a madadin ‘yan Majalisa 60 na PDP, inda PDP ɗin ke da mambobi 100 da ɗoriya.

“Ba zai yiwu a ce APC ce ke gudanar da ikon jam’iyyar PDP ba. Ba zai yiwu ‘yan APC su zama shugabannin PDP a Jihar Ribas da wasu jihohi 10 ba.

“Ya kamata duniya ta sani cewa ana ƙulle-ƙullen sai an ƙaƙaba APC a shugabannin jam’iyyar PDP na riƙo ba. Wani babban shiri ne suke ƙullawa.”

People are also reading