Home Back

Illar da yajin aiki ke yi wa ƙasa

bbc.com 2024/7/3
...

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun jingine yajin aikin da suka fara a ranar Litinin, bayan cimma yarjejeniya da gwamnatin tarayyar ƙasar a yammacin ranar.

Tun farko manyan ƙungiyoyin biyu sun kira yajin aikin ne bayan gaza cimma matsaya a kan albashin ma'aikata mafi ƙanƙanta a ƙasar.

An kwashe tsawon lokaci ana kai ruwa rana tsakanin gwamnatin tarayya da ƙungiyoyin ƙwadago na 'Nigeria Labour Congress da Trade Union Congress' a ƙasar ta Najeriya game da batun ƙarin albashin.

Sai dai abin ya ci tura bayan da ƙungiyoyin ƙwadagon suka zargi gwamnati da rashin mayar da hankali kan tattaunawar.

Sai dai jim kaɗan bayan fara yajin aikin a ranar Litinin, gwamnatin tarayya ta sake gayyatar ƙungiyoyin ƙwadagon zuwa teburin shawara, inda a ƙarshe ta yi alƙawarin cewa gwamnati za ta ƙara a kan naira 60,000 da ta gabatar a matsayin tayinta kan mafi ƙarancin albashin ma'aikaci a Najeriya.

Me ya sa gwamnati ke damuwa idan ma'aikata sun shiga yajin aikin?

...

Asalin hoton, PRESIDENCY NIGERIA

Dakta Ibrahim Shehu na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya ce manyan abubuwan da kan sa gwamnati ta damu idan ma'aikata suka fara yajin aiki biyu ne:

Zubar da mutuncin gwamnati: Ya ce "yajin aiki ba abu ne mai kyau ba, saboda haka idan gwamnati ta gaza magance matsala har ta kai ga an shiga yajin aiki, hakan zai zubar da martaba ko kuma kimar gwamnati".

Irin wannan a cewar malamin jami'ar kan rage kwarjini da kuma goyon bayan da gwamnati ke da shi a wurin al'umma.

Ya kuma bayyana cewa a tsari irin na mulkin dimokuraɗiyya wannan ba ƙaramar illa ba ce, domin hakan na iya yin tasiri a lokacin zaɓuka, ta yadda gwamnati ke iya rasa ƙuri'un wasu mutanen.

Tashin hankali: A duk lokacin da aka ce ma'aikata na yajin aiki, lamarin kan zamo barazana ga zaman lafiya da luma a a cikin ƙasa.

Dr Ibrahim ya ce a lokacin da yajin aiki ya tsananta: "idan wahala ta yi wahala mutane na iya shiga zanga-zanga, wadda za ta iya rikiɗewa zuwa tarzoma".

Ya bayyana cewa wannan zai iya zama babban tabo ga zaman lafiyar ƙasar, wanda kuma hakan zai sake komawa kan gwamnati, inda dole gwamnati za ta shiga wani yanayi na neman hanyoyin da za ta warware matsalar.

Illoli

Sai dai wani babban dalilin da ya sa gwamnati kan damu sosai shi ne irin illolin da yajin aikin ma'aikata kan yi wa tattali arziƙin ƙasa.

Dakta Ahmed Adamu na Jami'ar Nile da ke Abuja da kuma sun bayyana cewa yajin aiki na yin mummunan tasiri ga ƙasa da tattalin arziƙinta.

Illolin su ne:

Durƙusar da ayyuka

A duk lokacin da aka shiga yajin aiki akan rufe muhimman ma'aikatu da hukumomin gwamnati da masu zaman kansu.

Wannan kan yi illa matuƙa ga tattalin arziƙin ƙasa ta hanyar daƙile ayyukan da akan yi waɗanda ke taimakawa wajen tafiyar da lamurran ƙasa.

"Wannan kan janyo asara babba ga tattalin arziƙi ta hanyar rage samun kuɗi na gwamnati da ɗaiɗaikun al'umma".

Idan har ma'aikatu na kulle to duk wata hada-hada ta samun kuɗaɗe za su tsaya.

Durƙusar da sufuri

...

Wannan ɗaya ne daga cikin ɓangarorin da yajin aiki kan shafa, inda yakan yi tarnaƙi ga zirga-zirgar al'umma a faɗin ƙasa.

Hakan shi ma kan janyo asara mai yawa kasancewar ta hanyar sufuri ne akan isar da kayan da kamfanoni ke sarrafawa sannan ma'aikata ke iya zuwa warin aiki.

Misali, a ranar Litinin yajin aikin ƙungiyar ƙwadago ya yi tarnaƙi ga tashin jirage a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas, lamarin da ya sanya matafiya cikin ruɗani.

Rufe masana'antu

Akan yi asarar abubuwa da dama a duk lokacin da aka rufe masana'antu kasancewar ba za a iya sarrafa abubuwan buƙata da al'umma za su yi amfani da su ba.

Dakta Ibrahim ya ce "zai kai ga cewa ba a iya samar da yawan kayan da suka kamata a samar ba, waɗansu kuma za a yi asararsu saboda suna da saurin lalacewa idan ba a sarrafa su da wuri ba".

Illa ga ɓangaren ilimi

Makarantu kan rufe a lokacin da ake yajin aiki, hakan yakan sanya yara su zauna a gidaje.

Dr Ibrahim ya ce yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta shiga a Najeriya ya kai ga cewa an rufe wasu manya da ƙananan.

"Lamarin ya gurgunta komai, ya sa an bar yara kara-zube".

A cewar sa wannan kan yi illa sosai, musamman ganin cewa wasu daga cikin makarantui a Najeriya na rubuta jarrabawar kammala karatunsu ne na sakandare.

Rasa rayuka

...

Wani abu mai haɗari shi ne yadda ma'aikatan lafiya kan shiga cikin irin wannan yajin aiki, inda hakan kan kawo gagarumin cikas a kan yadda asibitoci ke gudanar da ayyukansu.

Dakta Ibrahim ya ce: "sai ka ga cewa an yi asarar rayuka sanadiyyar yajin aikin, kuma marasa lafiya da yawa kan tagayyara."

Kuɗin shiga

Yajin aiki kan taɓa tattalin arziƙin ƙasa ta hanyar rage yawan kuɗin shiga ga gwamnati.

Malamin ya bayyana cewa shiga yajin aiki kan shafi harajin da gwamnati ke tarawa kasancewar su kansu masu tara harajin suna cikin yajin aikin.

"Yakan shafi kuɗin shiga na gwamnati ta hanyar rage harajin da gwamnati ke samu," in ji shi.

People are also reading