Home Back

CNG: Manyan Matakai 3 da Tinubu Ya Dauka Na Janye Najeriya Daga Dogara da Man Fetur

legit.ng 2024/9/28

Manyan abubuwa uku da suka faru a cikin makon da ya gabata duk sun yi nuni ga turbar da gwamnatin Tinubu ta ke tafiya a kanta wajen sanya Najeriya a kan turbar makamashi mai dorewa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abdulaziz Abdulaziz, babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana ra'ayinsa kan wannan akidar ta sauya akalar kasar daga fetur zuwa CNG.

Kudurin Tinubu kan makamashi
Manufofin Bola Tinubu kan maye gurbin man fetur da iskar gas din CNG. Hoto: @officialABAT/X, Getty Images Asali: UGC

Jaridar The Cable ce ta wallafa ra'ayin Abdulaziz kamar haka:

Tinubu ya dauki matakai 3 kan makamashi

Matakin farko da Tinubu ya dauka shi ne ba da umarnin cewa ma’aikatu da hukumomin gwamnati su koma sayo ababen hawa da ke amfani da iskar gas din CNG.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Na biyu shi ne kaddamar da wasu muhimman ayyukan iskar gas guda uku a wani biki da aka yi a ranar Laraba ta yanar gizo.

Na uku a ciki shi ne sanarwar kawo motocin bas guda 530 masu amfani da CNG a fadin kasar, sai kuma rangadi da tawagar gwamnatin tarayya ta kai ga wani kamfani da ke kan gaba wajen samar da motocin CNG a Najeriya.

Me nene tasirin daukar wadannan matakan?

1. Amfani da motocin CNG

A taron majalisar zartarwa ta tarayya a ranar litinin, Tinubu ya sanar da wani kwakkwaran mataki da gwamnati ta dauka na dakatar da siyan motoci masu amfani da man fetur.

Wannan matakin, zai taimaka wajen rage kudaden da gwamnati ke kashewa wajen sayen fetur ga ababen hawan, musamman yanzu da aka ba hukumar Kwastam izinin sayen motoci 200 kirar Toyota Land Cruiser.

A yayin da Najeriya ta zama ta tara a jerin kasashe masu arzikin gas, ana ganin wannan umarnin zai taimaka wajen bunkasa sarrafa gas din kasar domin amfanin gida da waje.

2. Kaddamar da ayyuka 3 na gas

Kamar dai dama jira ake yi, domin kwanaki biyu bayan hana sayo motocin fetur, shugaban kasar ya kaddamar da wasu manyan ayyukan iskar gas guda uku.

Wannan aikin kuma na tare da hadin gwiwar samar da dala miliyan 500 ga Najeriya nan da shekaru 10 masu zuwa.

Ayyuka uku da Tinubu ya kaddamar su ne aikin fadada kamfanin sarrafa gas na AHL; kamfanin ANOH da kuma aikin bututun gas mai nisan kilomita 23.3 daga ANOH zuwa Obiafu-Obrikom-Oben (OB3).

Wadannan ayyukan za su karfafa samar da iskar gas ga bangaren samar da wutar lantarki, masana'antun gas, da sauran muhimman sassa na tattalin arziki.

3. Kaddamar da motocin bas guda 530

Ana tsaka da hakan ne gwamnati ta sanar da cewa za ta rarraba motocin bas guda 530 masu amfani da CNG domin maye gurbin masu amfani da man fetur.

Za a gudanar da jerin tarurruka na masu ruwa da tsaki na yankin Kudu maso Yamma wanda shirin Presidential Compressed Natural Gas Initiative (P-CNGi) ya shirya.

A yayin da aka kaddamar da shirin a shekarar da ta gabata, shirin P-NGi zai sauya shekar harkokin sufuri daga man fetur zuwa iskar gas a Najeriya.

Bisa ga ga karfafawar guiwar da suka samu daga gwamnati, kamfanoni irin su NIPCO, Matrix, BOVAS, Mikano, JET da Innoson sun zuba jari sosai a wajen samar da ababen hawa da janareta masu amfani da CNG.

Tinubu na da sha'awar harkar gas

A matsayinsa na wanda ya ke da sha'awar harkar makamashi, shugaban kasa Tinubu ya kasance mai burin fadada bincike da alkinta albarkatun iskar gas domin samun makamashi mai rahusa da tsabta.

Burinsa shi ne ya gaggauta bunkasa amfani da makamashin a cikin gida da kuma fitar da shi zuwa kasuwannin kasashen waje. Tun a yakin zabe ya bayyana hakan, yanzu kuma ya ke tabbatar da kudurinsa.

Wadannan matakai na baya-bayan nan, sun fito da manufofinsa na siyasa wajen ceto Najeriya da 'yan kasar daga matsalolin makamashi da kuma bunkasa ci gaban fannin.

Ayyuka da tsare-tsare 20 na Tinubu

Tun da fari, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da wasu ayyuka da tsare-tsare 20 a yayin da aka gudanar da taron majalisar zartarwar kasar.

Ayyukan sun haɗa da gina tituna da sayen motocin bas yayin da tsare-tsaren suka shafi wurare daban-daban da suka haɗa da gidaje, biza da kayan aikin zamani.

Asali: Legit.ng

People are also reading