Home Back

Samoa: Tinubu Zai Dauki Mataki Kan Daily Trust Game da Rahoton Yarjejeniyar da Aka Yi

legit.ng 2024/10/6
  • Yayin da rahoton yarjejeniyar Samoa ya bayyana, Gwamanti Tarayya ta shirya daukar mataki kan jaridar Daily Trust
  • Jaridar ce ta fara buga rahoton wanda ake zargin akwai halasta auren jinsi a cikin tsare-tsaren yarjejeniyar
  • Sai dai gwamnatin ya ƙaryata sanya hannu domin auren jinsi inda ta ce ta yi ne domin bunkasa tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta shirya daukar matakin kotu kan jaridar Daily Trust game da rahoton Samoa.

Gwamnatin ta ce rahoton an buga ne domin bats mata suna duba da yarjejejeniyar ba ta da alaka da abin da aka wallafa.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da hadimin Bola Tinubu, Daddy Olusegun ya wallafa a shafin X.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ya bayyana haka a yau Asabar 6 ga watan Yulin 2024 a Abuja.

Idris ya ce duk da Tinubu ya sakewa ƴan jaridu fuska wurin gudanar da ayyukansu amma sun fara wuce gona da iri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Daily Trust ta sha buga rahotannin karya ga Gwamanti Tarayya ana kawar da kai amma wannan ya wuce gona iri.

Karin bayani na tafe...

Asali: Legit.ng

People are also reading