Home Back

Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron OIC Karo Na 15

leadership.ng 2024/5/19
Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron OIC Karo Na 15 

A yau Asabar ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga bude taro karo na 15 na taron kolin kungiyar hadin kan kasashen musulmi OIC a Banjul, babban birnin kasar Gambiya.

Xi Jinping ya ce, kasar Sin da kasashen musulmi aminai ne na kwarai, kuma abokan hulda na dogon lokaci. A cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin da kasashen musulmi sun goya wa juna baya kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu da manyan damuwarsu. Hadin kai a zahiri ya haifar da sakamako mai kyau, kuma dangantakar abota ta ci gaba da inganta da kuma habaka, wanda ya zama abin koyi ga hadin gwiwar sauran kasashen. Kasar Sin a shirye take ta ci gaba da yin aiki tare da kasashen musulmi, wajen tabbatar da dadadden zumuncin dake tsakaninsu, da kara amincewa da juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin gwiwa a aikace, da kuma ba da babbar gudummawa wajen inganta gina al’ummar bil Adama mai makomar bai daya. (Mai fassara: Yahaya)

People are also reading