Home Back

InnalilLahi: Tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Lamorde Ya Rasu Yana da Shekaru 62

legit.ng 2024/9/28

An shiga jimami bayan rasuwar tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde a Masar bayan fama da jinya mai tsayi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Adamawa - Tsohon shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Lamorde ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 62.

Marigayin ya rasu ne a kasar Masar yayin da ya je domin yin jinya kamar yadda aka sanar da safiyar yau Lahadi 26 ga watan Mayu.

Premium Times ta tattaro cewa kafin rasuwar Lamorde, ya rike shugabancin hukumar EFCC daga shekarar 2011 zuwa 2015.

An haifi Lamorde a ranar 20 ga watan Disambar shekarar 1962 a jihar Adamawa inda ya shiga aikin dan sanda a shekarar 1986.

Karin bayani na tafe...

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

People are also reading