Home Back

Gobara ta kashe baki 'yan Asiya a Kuwaiti

dw.com 2024/7/4
Hoto: DPPI media/picture alliance

 Gobarar da ta tashi a unguwar Mangaf da ke kudu da babban birnin Kuwaitin, ta kuma yi sanadin jikkatar mutane 43. Shaidu sun ce gobarar ta tashi ne, a kasan benaye na wani gini da ma'aikatan Asiya ke zaune, kuma cikin sauri ta bazu zuwa saman benen. Wadanda abin ya shafa dai sun mutu ne sakamakon shakar hayakin da gobarar ta fitar, wanda har yanzu ba a tantance musabbabinta ba.Yanzu haka jami'an tsaro sun cafke wanda ya mallaki, benen a wani bangare na binciken yiwuwar sakaci, in ji ministan cikin gida na Kuwaitin a yayin ziyarar da ya kai  a wurin.

People are also reading