Goodluck Jonathan Ya Bayyana Abin da Ya Hana a Samu Cikakken Tsaro a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce babu yadda za a yi Najeriya ta samu tsaro idan jihohi ba su da ƴan sandan kansu.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wani taron yini guda kan ƴan sandan jihohi da majalisar wakilai ta shirya a Abuja ranar Litinin, 22 ga watan Afirilun 2024.
Jonathan ya ce al’amarin na da matuƙar muhimmanci, inda ya ce babu buƙatar a yi muhawara kan ko muna bukatar ƴan sandan jihohi ko a’a, sai dai a yi kan yadda za su gudanar da ayyukansu, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce yayin taron ƙasa na 2014 lokacin da batun ƴan sandan jihohi ya taso, duk wakilan da ke wurin sun nuna goyon bayansu.
Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana cewa yayin da ake tattaunawa kan batun ƴan sandan jihohi, dole ne kuma a ɗauki wasu matakai domin ganin ƙasar ta gyaru, rahoton The Whistler ya tabbatar.
Ya ce dole ne a sauya ayyukan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) tare da rage yin amfani da ƴan sanda a lokacin zaɓe.
Jonathan ya ce dole ne dokokin su yi ƙarfi ta yadda za su kawar da duk wata ƙofa da za ta ba ƴan siyasa damar yin amfani da ƴan sandan jihohi ta hanyar da ba ta dace ba domin muzgunawa abokan hamayyarsu.
A wani labarin kuma, kun ji cewa sufeto janar na ƴan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya bayyana matsayar rundunar ƴan sandan Najeriya kan shirin kirkiro da ƴan sandan jihohi.
Kayode Egbetpkun ya bayyana cewa ƙirƙirar ƴan sandan jihohi zai haifar da rikicin ƙabilanci, wanda hakan zai haifar da rashin jituwa a jihohin.
Asali: Legit.ng